Don haka Yusufu ya sami tagomashi a wurinsa, ya zama mai yi masa hidima. Fotifar kuma ya shugabantar da shi a bisa gidansa, da bisa dukan abin da yake da shi.
Amma Rut ta ce, “Kada ki yi ta roƙona in rabu da ke, ko in bar binki, gama inda za ki tafi, ni ma can zan tafi, inda kuma za ki zauna, ni ma can zan zauna. Mutanenki za su zama mutanena, Allahnki kuma zai zama Allahna.
Ita ce ta ce mana, ‘In kun yarda, ku bar ni in bi bayan masu girbin, ina kala.’ Haka ta yi ta kala tun da sassafe har yanzu ba hutu, sai dai 'yar shaƙatawar da ta yi kaɗan.”