Rut 2:19 - Littafi Mai Tsarki19 Surukarta kuma ta ce mata, “A ina kika yi kala yau? A gonar wa kika yi aiki? Albarka ta tabbata ga wannan mutum wanda ya kula da ke.” Sai ta faɗa mata sunan mutumin da ta yi kala a gonarsa, ta ce, “Sunan mutumin da na yi kala a gonarsa yau, Bo'aza.” Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 202019 Surukarta ta tambaye ta, “Ina kika yi kala a yau? Ina kika yi aiki? Albarka ta tabbata ga mutumin nan ta ya lura da ke!” Sai Rut ta faɗa wa surukarta game da wurin wanda ta yi ta aiki. Ta ce, “Sunan mutumin da na yi aiki da shi a yau Bowaz ne.” Faic an caibideil |