Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Rut 2:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Da lokacin cin abinci ya yi, sai Bo'aza ya kira Rut, ya ce, “Zo nan ki ci abinci, ki riƙa tsoma lomarki a ruwan inabin da aka surka.” Sai ta zo, ta zauna kusa da masu girbin. Shi kuwa ya ba ta tumun hatsi. Ta ci, ta ƙoshi har ta bar saura.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 A lokacin cin abinci Bowaz ya ce mata, “Zo nan. Ki ɗebo burodi ki tsoma cikin ruwan inabi.” Da ta zauna tare da masu girbin, sai ya ba ta gasasshe hatsi. Ta ci duk abin da take so har ta bar ragowa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Rut 2:14
17 Iomraidhean Croise  

suka kawo wa Dawuda da jama'arsa waɗannan kaya da abinci, wato gadaje, da tasoshi, da tukwane, da alkama, da sha'ir, da gari, da soyayyen hatsi, da wake, da waken barewa,


Ka shirya mini liyafa Inda maƙiyana duk za su iya ganina, Ka marabce ni, ka shafe kaina da mai, Ka cika tanduna fal da mai.


Amma mutum mai aminci yakan yi aikin aminci ya kuwa tsaya da ƙarfi a kan abin da yake daidai.


Ku ci abincinku tare da mayunwata, ku kuma shigo da matalauta, marasa mahalli a cikin gidajenku. Idan kuma kun ga wanda yake tsirara, ku sa masa sutura, kada kuma ku ɓoye fuskokinku ga 'yan'uwanku.


Duka kuwa suka ci suka ƙoshi, har suka kwashe ragowar gutsattsarin, cike da kwando goma sha biyu.


Zai sa ciyawa ta tsiro a saurukanku domin dabbobinku. Za ku ci ku ƙoshi.


Sa'ad da kuka ci, kuka ƙoshi, sai ku yabi Ubangiji Allahnku saboda kyakkyawar ƙasa mai albarka da ya ba ku.”


Rut ta ce, “Shugaba, kā yi mini alheri ƙwarai, gama kā ta'azantar da ni, kā yi wa baiwarka maganar alheri, ko da yake ni ba ɗaya daga cikin barorinka ba ce.”


Sa'ad da ta tashi, za ta yi kala, sai Bo'aza ya umarci barorinsa, ya ce, “Ku bar ta, ta yi kala a tsakanin tarin dammunan, kada ku hana ta.


Ta ɗauka, ta koma gari, ta nuna wa surukarta abin da ta kalato. Ta kuma kawo mata sauran abincin da ta ci ta ƙoshi har ta rage.


Wata rana ke nan, sai Yesse ya ce wa Dawuda, ɗansa, “Ka ɗauki wannan tumammen hatsi, da malmalar abinci goma, ka kai wa 'yan'uwanka da sauri a sansanin.


Sai Abigail ta yi sauri, ta ɗauki malmalar abinci guda metan, da salkar ruwan inabi biyu, da tumaki biyar da aka gyara, da soyayyen hatsi mudu uku, da nonnan 'ya'yan inabi guda ɗari, da kauɗar ɓaure guda metan, ta labta wa jakai.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan