Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Rut 1:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Amma Rut ta ce, “Kada ki yi ta roƙona in rabu da ke, ko in bar binki, gama inda za ki tafi, ni ma can zan tafi, inda kuma za ki zauna, ni ma can zan zauna. Mutanenki za su zama mutanena, Allahnki kuma zai zama Allahna.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Rut Amma Rut ta amsa, “Kada ki roƙe ni in bar ki ko in koma daga gare ki. Inda za ki, zan tafi, kuma inda za ki zauna, zan zauna. Mutanenki, za su zama mutanena kuma Allahnki, zai zama Allahna.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Rut 1:16
23 Iomraidhean Croise  

Amma Ittayi ya amsa wa sarki, ya ce, “Na rantse da zatin Ubangiji da darajar ubangijina, sarki, duk inda za ka tafi ko a mutu ko a yi rai zan tafi.”


Ki ji abin da zan faɗa, ya ke amaryar sarki, Ki manta da mutanenki da danginki.


A ko yaushe abokai sukan nuna ƙaunarsu, 'yan'uwa kuma, ai, don su ɗauki nawayar juna suke.


Ubangiji zai sāke yi wa jama'arsa Isra'ila jinƙai, ya zaɓe su su zama nasa. Zai sāke sa su zauna a ƙasarsu, baƙi ma za su zo su zauna tare da su.


Ya kuma ce wa Daniyel, “Hakika, Allahnka, Allahn alloli ne da Ubangijin sarakuna, mai bayyana asirai, gama ka iya bayyana wannan asiri.”


Domin haka ina ba da wannan umarni cewa, ‘Dukan jama'a, ko al'umma, ko harshe wanda zai yi saɓon Allah na Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, za a yanyanka su gunduwa gunduwa, a ragargaje gidajensu, gama ba wani allah wanda zai yi wannan irin ceto.’ ”


Yanzu ni, Nebukadnezzar, ina yabon Sarkin Samaniya, ina ɗaukaka shi, ina kuma girmama shi saboda dukan ayyukansa daidai ne, al'amuransa kuma gaskiya ne. Yakan ƙasƙantar da masu girmankai.”


Ubangiji ya ce, “Ni ne Ubangiji Allahnku Tun daga ƙasar Masar. Banda ni ba ku san wani Allah ba, Banda ni kuma ba wani mai ceto.


Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, a waɗannan kwanaki mutum goma daga kowace al'umma da kowane harshe za su kama kafa wurin Bayahude, su ce, ‘Ka yardar mana mu tafi tare da kai, gama mun ji Allah yana tare da ku.’ ”


Sai wani malamin Attaura ya zo ya ce masa, “Malam, zan bi ka duk inda za ka je.”


Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, don me, ba zan iya binka a yanzu ba? Ai, zan ba da raina saboda kai.”


Sai Bulus ya amsa ya ce, “Me ke nan kuke yi, kuna kuka kuna baƙanta mini rai? Ai, ni a shirye nake, ba wai a ɗaure ni kawai ba, har ma a kashe ni a Urushalima saboda sunan Ubangiji Yesu.”


Domin su da kansu suke ba da labarin irin ziyartarku da muka yi, da kuma yadda kuka rabu da gumaka, kuka juyo ga Allah, domin ku bauta wa Allah Rayayye na gaskiya,


Ubangiji kuwa ya kore mana dukan Amoriyawa waɗanda suke zaune a ƙasar, domin haka za mu bauta wa Ubangiji, gama shi ne Allahnmu.”


Waɗannan su ne waɗanda ba su taɓa ƙazantuwa da fasikanci ba, domin su tsarkaka ne. Su ne kuma suke bin Ɗan Ragon a duk inda ya je. Su ne kuma aka fanso daga cikin mutane a kan su ne nunan fari na Allah, da na Ɗan Ragon nan kuma,


Na'omi ta ce wa Rut, “Kin ga, 'yar'uwarki ta koma wurin mutanenta da wurin gumakanta, sai ki koma, ki bi 'yar'uwarki.”


Inda za ki rasu, ni ma can zan rasu, a binne ni. Idan na bar wani abu ya raba ni da ke, in dai ba mutuwa ba, to, Ubangiji ya yi mini hukunci mai zafi!”


Baran ya ce, “Ita 'yar Mowab ce wadda ta zo tare da Na'omi daga ƙasar Mowab.


Ya zama mai sanyaya miki rai, mai goyon tsufanki, gama surukarki wadda take ƙaunarki, wadda ta fiye miki 'ya'ya maza bakwai, ita ta haife shi.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan