Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Rut 1:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Suka sāke fashewa da kuka. Sai Orfa ta yi wa surukarta, sumba, ta yi bankwana da ita, amma Rut ta manne mata.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 A kan wannan suka sāke ɓarke da kuka. Sa’an nan Orfa ta sumbaci surukarta ta yi bankwana, amma Rut ta manne mata.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Rut 1:14
22 Iomraidhean Croise  

Don me ba ka bari na sumbaci 'ya'yana mata da maza na yi bankwana da su ba? Kai! Ka yi aikin wauta.


Da sassafe, Laban ya tashi ya sumbaci jikokinsa, da 'ya'yansa mata, ya sa musu albarka. Sa'an nan ya tashi ya koma gida.


Sa'an nan dukan jama'a suka haye Urdun, sarki kuma ya haye. Ya yi bankwana da Barzillai, ya sumbace shi, ya kuma sa masa albarka. Sai Barzillai ya koma gidansa.


Sai ya bar shanun noma, ya sheƙa gun Iliya, ya ce, “Bari in sumbaci mahaifina da mahaifiyata, in yi bankwana da su, sa'an nan in zo in bi ka.” Sa'an nan Iliya ya ce masa, “Koma, me na yi maka?”


A ko yaushe abokai sukan nuna ƙaunarsu, 'yan'uwa kuma, ai, don su ɗauki nawayar juna suke.


Waɗansu abokai ba su sukan ɗore ba, amma waɗansu abokai sun fi 'yan'uwa aminci.


Ubangiji zai sāke yi wa jama'arsa Isra'ila jinƙai, ya zaɓe su su zama nasa. Zai sāke sa su zauna a ƙasarsu, baƙi ma za su zo su zauna tare da su.


Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, a waɗannan kwanaki mutum goma daga kowace al'umma da kowane harshe za su kama kafa wurin Bayahude, su ce, ‘Ka yardar mana mu tafi tare da kai, gama mun ji Allah yana tare da ku.’ ”


Wanda duk ya fi son ubansa ko uwarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba. Wanda kuma ya fi son ɗansa ko 'yarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba.


Sai Yesu ya ce wa almajiransa, “Duk mai son bina, sai ya ƙi kansa, ya ɗauki gicciyensa, ya bi ni.


Da saurayin nan ya ji haka, sai ya tafi, yana baƙin ciki, don yana da arziki ƙwarai.


Amma waɗansu mutane suka koma wajensa suka ba da gaskiya, a cikinsu har da Diyonisiyas, ɗan majalisar Tudun Arasa, da wata mace mai suna Damarisa, da waɗansu dai haka.


Sai kuma ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku bauta masa. Ku manne masa, ku yi rantsuwa da sunansa.


Amma ku da kuka dogara ga Ubangiji Allahnku, a raye kuke har yau.


domin Dimas, saboda ƙaunar duniyar nan, ya yashe ni, ya tafi Tasalonika. Karaska ya tafi ƙasar Galatiya, Titus kuma ya tafi ƙasar Dalmatiya.


Amma mu ba a cikin waɗanda suke ja da baya su hallaka muke ba, mu a cikin masu bangaskiya muke, mai kai mu ga ceton rayukanmu.


za ku yi ta jira har su yi girma? Ai, ba zai yiwu ba, 'ya'yana. Ina baƙin ciki ƙwarai saboda abin da ya same ku, da yadda Ubangiji ya yi gāba da ni.”


Na'omi ta ce wa Rut, “Kin ga, 'yar'uwarki ta koma wurin mutanenta da wurin gumakanta, sai ki koma, ki bi 'yar'uwarki.”


Suka kama hanya zuwa ƙasar Yahudiya.


Amma Bo'aza ya ce mata, “An faɗa mini dukan abin da kika yi wa surukarki tun lokacin da mijinki ya rasu, da yadda kika bar iyayenki da ƙasarku, kika zo wurin mutanen da ba ki taɓa saninsu ba a dā.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan