Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Rut 1:12 - Littafi Mai Tsarki

12 Sai ku koma, 'ya'yana, gama na tsufa da yawa, ba kuma zan sami miji ba. Ko da a ce ina fata in yi aure, a ce ma zan yi aure a daren nan, in haifi 'ya'ya maza,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Ku koma gida ’ya’yana mata; na tsufa ainun da zan sāke samun wani miji. Ko ma na yi tsammani har yanzu ina da bege, ko ma na sami miji a wannan dare na kuma haifi ’ya’ya maza,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Rut 1:12
5 Iomraidhean Croise  

Sai Ibrahim ya yi ruku'u, ya yi dariya a zuciyarsa, ya ce wa kansa, “Za a haifa wa mai shekara ɗari ɗa? Zai yiwu Saratu mai shekara tasa'in ta haifi ɗa?”


Yahuza kuwa ya ce wa Tamar surukarsa, “Yi zaman gwauranci a gidan mahaifinki, har ɗana Shela ya yi girma,” gama yana jin tsoro kada shi kuma ya mutu kamar 'yan'uwansa. Saboda haka Tamar ta tafi ta zauna a gidan mahaifinta.


Kada a lasafta gwauruwa a cikin gwauraye, sai dai ta kai shekara sittin, ba ta yi aure fiye da ɗaya ba,


Amma Na'omi ta ce musu, “Ku koma, 'ya'yana, don me za ku tafi tare da ni? Ina da sauran 'ya'ya maza a cikina ne da za su zama mazajenku?


za ku yi ta jira har su yi girma? Ai, ba zai yiwu ba, 'ya'yana. Ina baƙin ciki ƙwarai saboda abin da ya same ku, da yadda Ubangiji ya yi gāba da ni.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan