10 suka ce mata, “A'a, mā tafi tare da ke wurin mutanenki.”
10 suka ce mata, “Za mu tafi tare da ke zuwa ga mutanenki.”
Ina abuta da duk waɗanda suke bauta maka, Da duk waɗanda suke kiyaye dokokinka.
Dubi irin martabar da amintattun jama'ar Ubangiji suke da ita! Ba abin da raina ya fi so, Sai in zauna tare da su.
Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, a waɗannan kwanaki mutum goma daga kowace al'umma da kowane harshe za su kama kafa wurin Bayahude, su ce, ‘Ka yardar mana mu tafi tare da kai, gama mun ji Allah yana tare da ku.’ ”
Amma Na'omi ta ce musu, “Ku koma, 'ya'yana, don me za ku tafi tare da ni? Ina da sauran 'ya'ya maza a cikina ne da za su zama mazajenku?
Suka kama hanya zuwa ƙasar Yahudiya.
Ya sa kuma ko waccenku ta yi aure, ta sami hutawa a gidan miji.” Sa'an nan ta yi bankwana da su ta sumbace su. Sai suka fashe da kuka,