Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Obadiya 1:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Jarumawanka za su firgita, ya Teman, Za a kashe kowane mutum daga dutsen Isuwa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Jarumawanki, ya Teman, za su razana, za a kashe kowane mutum a duwatsun Isuwa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Obadiya 1:9
19 Iomraidhean Croise  

'Ya'yan Elifaz su ne Teman, da Omar, da Zeho, da Gatam, da Kenaz.


Sa'ad da uku daga cikin abokan Ayuba, wato Elifaz daga birnin Teman, da Bildad daga ƙasar Shuwa, da Zofar daga ƙasar Na'ama, suka ji labarin irin yawan wahalar da Ayuba yake sha, sai suka kama hanya suka tafi su ziyarce shi, su ta'azantar da shi.


Domin haka, ku ji shirin da ni Ubangiji na yi wa Edom, da abin da nake nufin yi wa mazaunan Teman. Hakika za a tafi da su, har da ƙanana na garken tumaki, zan kuma sa wurin kiwonsu ya zama ƙeƙuwa saboda su.


Wani zai tashi da sauri, ya yi sama kamar gaggafa. Zai buɗe fikafikansa a kan Bozara. Zukatan sojojin Edom za su zama kamar zuciyar macen da take naƙuda.”


Ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya faɗa a kan Edom, “Ba hikima kuma a cikin Teman? Shawara ta lalace a wurin masu basira? Hikima ta lalace ne?


domin haka ni Ubangiji Allah zan hukunta Edom. Zan kashe mutanenta da dabbobinta, zan maishe ta kufai. Za a kashe su da takobi, tun daga Teman har zuwa Dedan.


Saboda haka zan aukar da wuta a kan Teman, Ta ƙone kagarar Bozara.”


Ko sojojin da suka fi jaruntaka duka ma, Za su gudu tsirara a ran nan.” Ubangiji ne ya faɗa.


Isra'ilawa za su hau Dutsen Sihiyona, su cece shi, Za su mallaki dutsen Isuwa, Ubangiji ne Sarki.


“Idan ɓarayi sun shiga gidanki, Idan kuma 'yan fashi sun shiga gidanki da dare, Yaya za su washe ki? Za su sace abin da ya ishe su ne kaɗai, Idan kuma ɓarayin 'ya'yan inabi sun shiga gonar inabinki, Za su bar miki kala kurum.


Sojojinki kamar mata suke a tsakiyarki! An buɗe wa maƙiyanki ƙofofin ƙasarki. Wuta za ta cinye madogaran ƙofofinki.


Daga Edom Allah ya zo, Daga dutsen Faran Mai Tsarki yake tahowa. Ɗaukakarsa ta rufe sammai, Duniya kuwa ta cika da yabonsa.


kada ku tsokane su, gama ko wurin sa ƙafa a ƙasarsu ba zan ba ku ba, gama na riga na ba Isuwa ƙasar tuddai ta Seyir.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan