Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Obadiya 1:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Ni Ubangiji na ce, “A ranar da zan hukunta Edom, Zan hallaka masu hikimarka, Zan shafe hikima daga dutsen Isuwa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 “A wannan rana,” in jin Ubangiji, “zan hallaka masu hikimar Edom, zan shafe mutane masu fahima a duwatsun Isuwa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Obadiya 1:8
8 Iomraidhean Croise  

Ubangiji yakan sassoke manufofin sauran al'umma, Yakan hana su aikata shirye-shiryensu.


Shugabannin birnin Zowan wawaye ne! Mutanen Masar mafi hikima za su ba da gurguwar shawara! Ta ƙaƙa za su iya dosar sarki su faɗa masa, cewa su ne suka gāji masana da sarakuna na dā can?


Sarkin Masar, ina mashawartan nan naka masu hikima? Watakila za su iya faɗa maka shirye-shiryen da Ubangiji Mai Runduna ya yi domin Masar.


Zan warware shirye-shiryen Masarawa in sa ku karai. Za su roƙi taimako ga gumakansu, za su je kuma su yi shawara da mabiyansu, su kuma nemi shawarar kurwar matattu.


Don haka zan firgita su ba zato ba tsammani, da dūka a kai a kai. Waɗanda suke da hikima za su zama wawaye, dukan wayon nan nasu kuwa ba zai amfana musu kome ba.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan