Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Obadiya 1:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Waɗanda kake amana da su, Za su kore ka daga ƙasarka. Mutanen da suke amana da kai, Za su yaudare ka, Su ci ka da yaƙi. Abokan nan naka da kake ci tare da su za su kafa maka tarko, Sa'an nan su ce, ‘Ina dukan wayon nan nasa?’ ”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Dukan waɗanda kike tarayya da su, za su kore ki zuwa iyaka; abokanki kuma za su yaudare ki, su kuma sha ƙarfinki; waɗanda suke cin abincinki, za su sa miki tarko, amma ba za ki gane ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Obadiya 1:7
16 Iomraidhean Croise  

Ka ji ƙaina ya Ubangiji, ka maido mini da lafiyata, Zan kuwa sāka wa magabtana!


Har da shaƙiƙin abokina, Wanda na fi amincewa da shi. Wanda muke ci tare, ya juya yana gāba da ni.


Rassan itatuwa sun bushe sun kakkarye, mata kuwa sun tattara, don su riƙa hura wuta da su. Da yake jama'a ba su gane kome ba, Allah Mahaliccinsu ba zai ji tausayinsu ba, ba zai nuna musu jinƙai ba.


Na ji mutane da yawa suna sa mini laƙabi cewa, ‘Razana ta kowace fuska,’ Suna cewa, ‘Mu la'anta shi! Mu la'anta shi!’ Har ma da abokaina shaƙiƙai Suna jira su ga fāɗuwata. Suka ce, ‘Watakila a ruɗe shi, Sa'an nan ma iya rinjayarsa Mu ɗauki fansa a kansa.’


Dukan masu ƙaunarku sun manta da ku, Ba su ƙara kulawa da ku, Domin na yi muku bugu irin na maƙiyi. Na yi muku horo irin na maƙiyi marar tausayi, Domin laifofinku masu girma ne, Domin zunubanku da yawa suke.


Ga shi, dukan matan da suka ragu a gidan Sarkin Yahuza, za a kai su wurin sarakunan Sarkin Babila, suna cewa, “ ‘Aminanka sun ruɗe ka, Sun rinjaye ka. Yanzu sun ga ƙafafunka sun nutse cikin laka, Sai suka rabu da kai.’


Ya ke da kike kufai marar kowa, Me kike nufi da kika ci ado da mulufi, Kike caɓa ado da kayan zinariya, Kika sa wa idanunki tozali ram? Kin yi kwalliyarki a banza, Abokan sha'anin karuwancinki sun raina ki, Ranki suke nema.


Ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya faɗa a kan Edom, “Ba hikima kuma a cikin Teman? Shawara ta lalace a wurin masu basira? Hikima ta lalace ne?


“Na kira masoyana, amma suka yaudare ni, Firistocina da dattawana a cikin birni sun hallaka Saboda neman abincin da za su ci su rayu.


Naƙudar haihuwarsa ta zo, Amma shi wawan yaro ne, Bai fito daga mahaifar ba.


Ifraimu kamar kurciya take, marar wayo, marar hankali, Takan tafi Masar da Assuriya neman taimako.


Ba dukanku nake nufi ba. Na san waɗanda na zaɓa. Wannan kuwa duk domin a cika Nassi ne cewa, ‘Wanda yake cin abincina ya tasar mini.’


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan