Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Obadiya 1:5 - Littafi Mai Tsarki

5 “Idan ɓarayi sun shiga gidanki, Idan kuma 'yan fashi sun shiga gidanki da dare, Yaya za su washe ki? Za su sace abin da ya ishe su ne kaɗai, Idan kuma ɓarayin 'ya'yan inabi sun shiga gonar inabinki, Za su bar miki kala kurum.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 “In ɓarayi suka zo miki, in kuma ’yan fashi suka shigo gidan da dare, kash, bala’i zai jira ki ba abin da suke so ne kawai za su sata ba? In kuma masu tsinka ’ya’yan inabi suka zo miki, ba sukan bar ’ya’yan inabi kaɗan ba?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Obadiya 1:5
13 Iomraidhean Croise  

“An kashe darajarki, ya Isra'ila, a kan tuddanki! Jarumawan sojojinmu sun fāɗi!


Ya Sarkin Babila, kai da kake tauraron asubahi mai haske, ka fāɗo daga sama. A dā ka ci al'ummai da yaƙi amma yanzu an fyaɗa ka ƙasa.


Isra'ila kuma za ta zama kamar itacen zaitun wanda aka karkaɗe 'ya'yansa, aka bar biyu ko uku kawai a ƙwanƙolin itacen, ko kuma aka bar huɗu ko biyar a rassansa. Ni Ubangiji Allah na Isra'ila, na faɗa.”


Wannan shi ne abin da zai sami kowace al'umma ko'ina a duniya. Zai zama kamar ƙarshen kaka sa'ad da aka karkaɗe zaitun daga kowane itace, aka kuma gama tsinke 'ya'yan inabi daga kurangar inabi.


Idan masu tsinkar 'ya'yan inabi sun zo wurinka Ba za su rage abin kala ba? Idan kuma ɓarayi sun zo da dare, Za su ɗauki iyakacin abin da suke so kurum.


Ga yadda aka karya gudumar dukan duniya! Ga yadda Babila ta zama abar ƙyama ga sauran al'umma!


Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Za a kalace ringin Isra'ila sarai, kamar yadda ake wa inabi, Ka miƙa hannunka a kan rassanta kamar mai tsinkar 'ya'yan inabi.”


Urushalima wadda take cike da mutane a dā, Yanzu tana zaman kaɗaici! Tana zama kamar mace wadda mijinta ya rasu, Ita wadda dā ta zama babba a cikin sauran al'ummai! Ita wadda take a dā sarauniya a cikin larduna, Ta zama mai biyan gandu!


Jarumawanka za su firgita, ya Teman, Za a kashe kowane mutum daga dutsen Isuwa.


Tawa ta ƙare, gama na zama kamar lokacin da aka gama tattara amfanin gona, Kamar lokacin da aka gama kalar 'ya'yan inabi, Ba nonon inabi da za a tsinka, a ci, Ba kuma 'ya'yan ɓaure da suka harba wanda raina yake so.


Wannan shi ne birnin da yake da harka, mai zaman lafiya, Wanda yake ce wa kansa, “Ba wani sai ni.” Ga shi, ya zama kufai, Wurin zaman dabbobi! Duk wanda ya wuce ta wurin, Zai yi tsaki, ya kaɗa kai.


Sa'ad da kuka girbe gonar inabinku kada kuma ku yi kala, sai ku bar wa baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske.


za su tsaya a can nesa, don tsoron azabarta, su ce, “Kaitonka! Kaitonka, ya kai babban birni! Ya kai birni mai ƙarfi, Babila! A sa'a ɗaya hukuncinka ya auko.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan