Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Obadiya 1:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Girmankanki ya yaudare ki, Kina zaune a kagara, a kan dutse, Wurin zamanki yana can ƙwanƙolin duwatsu. Don haka a zuciya kike cewa, ‘Wa zai saukar da ni ƙasa?’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Fariyar zuciyarki ta yaudare ki, ke da kike zama can bisa duwatsu kika kuma yi gidanki a kan ƙwanƙoli, ke da kike ce wa kanki, ‘Wa zai iya saukar da ni ƙasa?’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Obadiya 1:3
21 Iomraidhean Croise  

Saboda haka Isuwa ya zauna a ƙasar Seyir ta tuddai. Isuwa shi ne Edom.


Ya kuma kashe Edomawa dubu goma (10,000) a Kwarin Gishiri, sa'an nan ya ƙwace Sela, ya ba ta suna Yokteyel, haka ake kiranta har wa yau.


Amma Amaziya ya yi ƙarfin hali ya shugabanci jama'arsa, suka tafi Kwarin Gishiri, suka karkashe mutanen Seyir dubu goma (10,000).


Mutanen Yahuza kuma suka kama waɗansu mutum dubu goma (10,000) da rai, suka kai su a ƙwanƙolin dutse, suka yi ta tunkuɗa su ƙasa daga ƙwanƙolin dutsen, duka suka yi kaca-kaca.


Mai yiwuwa ne ya ƙasaita, ya zama kamar hasumiya a sararin sama. Ya ƙasaita har kansa ya taɓa gizagizai.


Girmankai jagora ne zuwa ga hallaka, fāriya kuwa zuwa ga fāɗuwa.


Ba wanda za a girmama sai mai tawali'u, mutum mai girmankai kuwa yana kan hanyar hallaka.


Girmankan mutum zai jawo masa ƙasƙanci, amma za a girmama mai tawali'u.


Mutanen Yahuza sun ce, “Mun ji irin fāriyar da mutanen Mowab suke yi. Mun sani su masu girmankai ne, masu ruba, amma fankamarsu ta banza ce.”


Ga shi, ina gāba da ku, ya ku mazaunan kwarin, Ya dutsen da yake a fili,’ in ji Ubangiji. ‘Ku da kuke cewa, wa zai iya gangarowa wurinku, Ko kuwa wa zai shiga wurin zamanku?


Ni Ubangiji, na ce kada ku ruɗi kanku da cewa Kaldiyawa ba za su dawo ba, gama ba shakka za su zo.


“Ku mazaunan Mowab, ku bar garuruwanku, Ku tafi, ku zauna a kogwanni, Ku zama kamar kurciya wadda take yin sheƙarta a bakin kwazazzabo.


Tsoronki da ake ji da girmankanki sun ruɗe ki, Ke da kike zaune a kogon dutse, a kan tsauni, Ko da yake kin yi gidanki can sama kamar gaggafa, Duk da haka zan komar da ke ƙasa, Ni Ubangiji na faɗa.”


Me ya sa kuke taƙama da ƙarfinku, Ƙarfinku da yake ƙarewa, ku mutane marasa aminci? Kun dogara ga dukiyarku, Kuna cewa, ‘Wane ne zai iya gāba da mu?’


A wurin yawan kasuwancinka, Ka yi rikici da yawa har ka yi zunubi. Don haka na jefar da kai daga dutsen Allah Kamar ƙazantaccen abu. Na hallaka ka daga tsakiyar duwatsu na wuta, Kai mala'ikan tsaro.


Edomawa, wato zuriyar Isuwa, sun ce, “An rurrushe garuruwanmu, amma za su sāke gina su.” Sa'an nan Ubangiji zai amsa, ya ce, “To, su gina mana, ai, zan sāke rurrushe su. Mutane za su ce da ƙasarsu, ‘Ƙasar mugaye, da al'ummar da Ubangiji yake fushi da ita har abada.’ ”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan