Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Obadiya 1:21 - Littafi Mai Tsarki

21 Isra'ilawa za su hau Dutsen Sihiyona, su cece shi, Za su mallaki dutsen Isuwa, Ubangiji ne Sarki.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 Masu kawo ceto za su haura zuwa Dutsen Sihiyona don su yi mulkin duwatsun Isuwa. Ubangiji ne zai yi mulki.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Obadiya 1:21
37 Iomraidhean Croise  

Sai Ubangiji ya ce mata, “Al'umma biyu suke a cikin mahaifarki, mutum biyu da za ki haifa, za su rabu da juna, ɗayan zai fi ɗayan ƙarfi, babban zai bauta wa ƙaramin.”


Saboda haka Ubangiji ya ba jama'ar Isra'ila maceci, suka kuwa kuɓuta daga ƙangin Suriyawa, suka zauna a gidajensu lafiya kamar dā.


Saboda haka ka bar abokan gābansu su ci su, mallake su. A wahalarsu sun yi kira gare ka domin taimako, Ka kuwa amsa musu daga Sama. Ta wurin jinƙanka mai yawa ka aiko musu da shugabanni, Waɗanda suka kuɓutar da su daga maƙiyansu.


Sauran al'umma za su ji tsoron Ubangiji, Dukan sarakunan duniya za su ji tsoron ikonsa.


Ubangiji Sarki ne, Yana mulki a kan al'ummai.


Masu girmankai duka za su rusuna masa, 'Yan adam duka za su rusuna masa, Dukan waɗanda aka ƙaddara musu mutuwa.


Allah sarki ne na duniya duka, Ku yabe shi da waƙoƙi!


Da ma sauran al'umma su yi murna, su raira waƙa ta farin ciki, Domin kana yi wa jama'a shari'a ta adalci, Kana kuma bi da dukan sauran al'umma.


Za su zama alamu na kasancewar Ubangiji Mai Runduna a Masar. Sa'ad da aka zalunci mutanen da suke can, za su yi kira ga Ubangiji su nemi taimako, zai aika musu wanda zai kuɓutar da su.


Wata zai duhunta, rana ba za ta ƙara haskakawa ba, domin Ubangiji Mai Runduna yake sarauta. Zai yi mulki a Urushalima a kan Dutsen Sihiyona, shugabannin jama'a za su dubi ɗaukakarsa.


Waɗanda suke da hikima za su haskaka kamar sararin sama, waɗanda kuma suka juyar da mutane da yawa zuwa adalci, za su zama kamar taurari har abada abadin.


Sa'an nan baƙin ƙarfen, da yumɓun, da tagullar, da azurfar, da zinariyar suka ragargaje gaba ɗaya, duka suka zama kamar ƙaiƙayi na masussuka da kaka. Iska kuwa ta kwashe su ta tafi da su, har ba a iya ganin ko alamarsu. Amma wannan dutse da ya buge mutum-mutumin ya girke, ya zama babban dutse ya cika duniya duka.


A kwanakin waɗannan sarakuna, Allah na Sama zai kafa wani mulki wanda ba zai taɓa rushewa ba har abada, ba kuma za a gādar da shi ga waɗansu mutane ba. Wannan mulki zai ragargaje dukan waɗannan mulkoki, ya kawo ƙarshensu. Wannan mulki zai dawwama har abada.


Aka kuwa danƙa masa mulki, da ɗaukaka, da sarauta, Domin dukan jama'a, da al'ummai, da harsuna su bauta masa. Mulkinsa, madawwamin mulki ne, Wanda ba zai ƙare ba. Sarautarsa ba ta tuɓuwa.”


Sa'an nan za a ba da sarauta da girman dukan mulkokin duniya ga tsarkaka na Maɗaukaki. Mulkinsa madawwamin mulki ne. Dukan sarakunan duniya za su bauta masa, su kuma yi masa biyayya.’


Amma dukan waɗanda suka nemi Ubangiji za su tsira. Kamar yadda Ubangiji ya ce, Akwai waɗanda suke a Dutsen Sihiyona da Urushalima Da za su tsira, Waɗannan da Ubangiji ya zaɓa za su tsira.”


Zan sa guragu su wanzu, Korarru kuwa su zama al'umma mai ƙarfi, Ni, Ubangiji, zan yi mulkinsu a Sihiyona har abada.


A ranar, Ubangiji zai zama Sarkin Duniya duka, zai kuma zama shi ne Ubangiji shi kaɗai, ba wani suna kuma sai nasa.


Mulkinka yă zo, A aikata nufinka a duniya kamar yadda ake yi a Sama.


Kada ka kai mu wurin jaraba, Amma ka cece mu daga Mugun.’


ku ci ku sha tare da ni a mulkina, ku kuma zauna a kursiyai, kuna hukunta kabilan nan goma sha biyu na Isra'ila.


Ka kula da kanka da kuma koyarwarka. Ka nace da haka, domin ta yin haka za ka ceci kanka da masu sauraronka.


to, yă dai tabbata, kowa ya komo da mai zunubi a hanya daga bauɗewarsa, ya kuɓutar da ran mai zunubin nan ke nan daga mutuwa, ya kuma rufe ɗumbun zunubansa.


Sa'an nan mala'ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji waɗansu muryoyi masu ƙara a Sama, suna cewa, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa, shi kuma zai yi mulki har abada abadin.”


Sai na ji kamar wata sowar ƙasaitaccen taro, kamar ƙugin ruwa mai gudu, kamar aradu mai ƙara, suna cewa, “Halleluya! Gama Ubangiji Allahnmu Maɗaukaki shi ne yake mulki.


Sa'an nan na ga kursiyai, da waɗanda aka bai wa ikon hukunci, zaune a kai. Har wa yau, kuma na ga rayukan waɗanda aka fille wa kai saboda shaidar da suka yi wa Yesu, da kuma Maganar Allah, ba su kuwa yi wa dabbar nan da siffarta sujada ba, ba su kuma yarda a yi musu alamarta a goshinsu ko a hannunsu ba, sun sāke rayuwa, sun yi mulki tare da Almasihu har shekara dubu.


Sa'an nan Ubangiji ya naɗa musu mahukunta masu ƙarfi da suka cece su daga waɗanda suka washe su.


Amma sa'ad da Isra'ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, sai Ubangiji ya ta da Otniyel, ɗan Kenaz, ƙanen Kalibu don ya ceci Isra'ilawa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan