Obadiya 1:20 - Littafi Mai Tsarki20 Rundunar masu zaman talala na Isra'ilawa Za su mallaki Kan'aniyawa har zuwa Zarefat. Masu zaman talala na Urushalima da suke a Sefarad Za su mallaki biranen Negeb. Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 202020 Wannan ƙungiyar Isra’ilawan da aka kwashe zuwa bauta da suke a Kan’ana za su mallaki ƙasar har zuwa Zarefat; waɗannan da aka kwashe zuwa bauta daga Urushalima da suke a Sefarad za su mallaki garuruwan Negeb. Faic an caibideil |
Za a sayi gonaki da kuɗi, a sa hannu a kan sharuɗa, a hatimce su a gaban shaidu, a ƙasar Biliyaminu da wuraren da suke kewaye da Urushalima, da cikin garuruwan Yahuza, da na garuruwan ƙasar tudu, da a garuruwan kwaruruka, da a garuruwan Negeb, gama zan komar wa mutane da wadatarsu a ƙasarsu, ni Ubangiji na faɗa.”