Obadiya 1:19 - Littafi Mai Tsarki19 Isra'ilawan da yake Negeb za su mallaki dutsen Isuwa, Waɗanda suke a filaye na Yahuza za su mallaki ƙasar Filistiya. Isra'ilawa za su mallaki yankin ƙasar Ifraimu da Samariya, Jama'ar Biliyaminu za su mallaki Gileyad. Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 202019 Mutane daga Negeb za su mamaye duwatsun Isuwa, mutane kuma daga gindin tuddai za su mallaki ƙasar Filistiyawa. Za su mamaye filayen Efraim da Samariya, Benyamin kuwa zai mallaki Gileyad. Faic an caibideil |
Za a sayi gonaki da kuɗi, a sa hannu a kan sharuɗa, a hatimce su a gaban shaidu, a ƙasar Biliyaminu da wuraren da suke kewaye da Urushalima, da cikin garuruwan Yahuza, da na garuruwan ƙasar tudu, da a garuruwan kwaruruka, da a garuruwan Negeb, gama zan komar wa mutane da wadatarsu a ƙasarsu, ni Ubangiji na faɗa.”