Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Obadiya 1:17 - Littafi Mai Tsarki

17 “Amma za a sami waɗanda za su tsira daga Dutsen Sihiyona, Dutsen zai zama wuri ne mai tsarki. Jama'ar Yakubu za ta mallaki mallakarta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 Amma a kan Dutsen Sihiyona za a sami ceto; Dutsen zai zama mai tsarki, gidan Yaƙub kuma zai mallaki gādonsa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Obadiya 1:17
25 Iomraidhean Croise  

Gama zai ceci Sihiyona, Ya sāke gina garuruwan Yahuza, Jama'arsa za su zauna a wurin, su mallaki ƙasar.


Gama Ubangiji mai adalci ne, zai ceci Urushalima da dukan wanda ya tuba a can.


Lokaci na zuwa sa'ad da Ubangiji zai sa kowane tsiro da kowane itacen da take a ƙasar su girma su yi kyau. Dukan jama'ar Isra'ila waɗanda suka ragu za su yi fāriya, su yi murna saboda amfanin da ƙasar take bayarwa.


Ina kawo ranar nasara kusa, Ba ta da nisa ko kaɗan. Nasarata ba za ta yi jinkiri ba. Zan ceci Urushalima, Zan kuma kawo ɗaukaka ga Isra'ila a can.”


Dukan mutanenki za su yi abin da yake daidai, Za su kuwa mallaki ƙasar har abada. Ni na dasa su, ni na yi su Domin su bayyana girmana ga duka.


Zan sa wa Isra'ilawa waɗanda suke na kabilar Yahuza albarka, zuriyarsu kuma za su mallaki ƙasata da duwatsuna. Zaɓaɓɓun mutanena waɗanda suke bauta mini za su zauna a can.


Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, “Nan gaba za su sāke yin magana a ƙasar Yahuza da biranenta a sa'ad da na mayar musu da dukiyarsu. “ ‘Ubangiji ya sa maka albarka, Ya wurin zaman adalci, Ya tsattsarkan tudu!’


Ba waɗansu daga cikin mutanen Yahuza da suka ragu, waɗanda suka zo Masar da zama, da za su tsere ko su rayu. Ba wani daga cikinsu da zai koma Yahuza inda suke marmarin komawa da zama, ba wanda zai koma, sai dai 'yan gudun hijira.”


‘Yan kaɗan ne za su tsere wa takobi, za su kuwa koma daga ƙasar Masar zuwa ƙasar Yahuza. Sauran mutanen Yahuza da suka ragu, waɗanda suka zo Masar da zama, za su sani ko maganar wa za ta cika, tasu ko kuwa tawa.


Ni Ubangiji na ce, Kada ka ji tsoro, ya bawana Yakubu, Gama ina tare da kai. Zan hallaka dukan sauran al'umma sarai inda na kora ka. Amma ba zan hallaka ka sarai ba. Zan hukunta ka yadda ya kamata, Ba zan bar ka ba hukunci ba.”


Zan kuma sa mutanena, Isra'ila, su yi tafiya a kanku, za ku zama gādonsu, ba za ku ƙara kashe 'ya'yansu ba.


Idan akwai waɗanda suka tsere, za a same su a kan duwatsu kamar kurciyoyin kwaruruka, suna baƙin ciki dukansu, kowa yana baƙin ciki saboda laifinsa.


Amma tsarkaka na Maɗaukaki za su karɓi mulki, su kuwa riƙe mulkin har abada abadin.


Amma dukan waɗanda suka nemi Ubangiji za su tsira. Kamar yadda Ubangiji ya ce, Akwai waɗanda suke a Dutsen Sihiyona da Urushalima Da za su tsira, Waɗannan da Ubangiji ya zaɓa za su tsira.”


“Sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji Allahnku, Wanda yake zaune a Sihiyona, tuduna tsattsarka. Urushalima kuma za ta tsarkaka, Sojojin abokan gāba ba za su ƙara ratsawa ta cikinta ba.


Kun kwashe azurfata da zinariyata kun kuma washe taskata, kun kai cikin haikalinku.


Ina dai kallon mulkin nan mai zunubi. Zan hallaka su daga duniya, Amma ba zan hallaka dukan jama'ar Yakubu ba.


Gama za a yi shuka da salama. Kurangar inabi za ta yi 'ya'ya, ƙasa kuma za ta ba da amfani, za a yi isasshen ruwan sama. Ni kuwa zan sa sauran jama'an nan su ci moriyar abubuwan nan duka.


Zan koma wurin Sihiyona, in zauna a tsakiyar Urushalima. Za a ce da Urushalima birnin gaskiya, da kuma dutsen Ubangiji Mai Runduna, tsattsarkan dutse.


Amma ko kaɗan ba wani abu marar tsarki da zai shiga cikinsa, ko wani mai aikata abin ƙyama ko ƙarya, sai dai waɗanda aka rubuta sunayensu a Littafin Rai na Ɗan Ragon kaɗai.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan