Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Obadiya 1:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Kamar yadda kuka sha hukunci a kan tsattsarkan dutsena, Haka dukan sauran al'umma za su yi ta sha. Za su sha, su yi tangaɗi, Su zama kamar ba su taɓa kasancewa ba.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Kamar yadda kuka sha a kan tuduna mai tsarki, haka dukan al’ummai za su yi ta sha, za su sha, su kuma sha su zama sai ka ce ba su taɓa kasancewa ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Obadiya 1:16
13 Iomraidhean Croise  

Allah ya ce, “Na daɗe na yi shiru, Ban amsa wa jama'ata ba. Amma yanzu lokaci ya yi da zan yi wani abu, Na yi ƙara kamar matar da take fama da zafin naƙuda.


Ubangiji ya ce, “Ga shi, waɗanda ba a shara'anta su ga shan ƙoƙon hukunci ba, za su sha shi, to, kai za ka kuɓuta? Ba za ka kuɓuta ba, amma lalle za ka sha shi!


Ki yi farin ciki, ki yi murna, ke Edom, Wadda kike zaune cikin ƙasar Uz. Amma fa za a ba ki ƙoƙo ki sha, Ki bugu har ki yi tsiraici.


“Sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji Allahnku, Wanda yake zaune a Sihiyona, tuduna tsattsarka. Urushalima kuma za ta tsarkaka, Sojojin abokan gāba ba za su ƙara ratsawa ta cikinta ba.


“Sun zo don su yi kama-karya. Ana jin tsoronsu tun ma kafin su zo. Sun tattara bayi kamar yashi.


Don lokaci ya yi da za a fara shari'a ta kan jama'ar Allah. In kuwa ta kanmu za a fara, to, me zai zama ƙarshen waɗanda ba su bi bisharar Allah ba?


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan