Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Obadiya 1:15 - Littafi Mai Tsarki

15 “Ranar da ni Ubangiji zan shara'anta al'ummai duka ta zo kusa, Ke, Edom, abin da kika yi, Shi ne za a yi miki. Ayyukanki za su koma a kanki.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

15 “Ranar Ubangiji ta yi kusa don dukan al’ummai. Kamar yadda kuka yi, haka za a yi muku; ayyukanku za su koma a kanku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Obadiya 1:15
28 Iomraidhean Croise  

Amma da Esta ta zo wurin sarki, sai sarki ya ba da umarni a rubuce, cewa mugun makircin nan da Haman ya shirya wa Yahudawa ya koma a kansa. Shi da 'ya'yansa maza aka rataye su a bisa gumagumai.


“Me ya sa Allah bai tsai da ranar da zai yi shari'a ba? Me ya sa ba ya tsai da ranar adalci ga Waɗanda suka bauta masa?


Babila, za a hallaka ki! Mai farin ciki ne shi wanda ya sāka miki Bisa ga abin da kika yi mana.


Zunuban mutum tarko ne, komar zunubinsa ce take kama shi.


Ga abin da Ubangiji ya faɗa a kan mugayen maƙwabtan Isra'ila waɗanda suka taɓa gādon da ya ba jama'arsa Isra'ila su gada. “Saboda haka zan tumɓuke su daga cikin ƙasarsu. Zan kuma tumɓuke mutanen Yahuza daga cikinsu.


Ubangiji ya ce, “Ga shi, waɗanda ba a shara'anta su ga shan ƙoƙon hukunci ba, za su sha shi, to, kai za ka kuɓuta? Ba za ka kuɓuta ba, amma lalle za ka sha shi!


“Ku kirawo 'yan baka, dukan waɗanda sukan ja baka, su faɗa wa Babila. Ku kafa sansani kewaye da ita, kada ku bar kowa ya tsira. Ku sāka mata bisa ga dukan ayyukanta, gama ta raina Ubangiji Mai Tsarki na Isra'ila.


Gama mai hallakarwa ya auka wa Babila, An kama sojojinta, An kuma kakkarya bakunansu, Gama Ubangiji shi Allah ne, mai sakayya, Zai yi sakayya sosai.


Gama ranar ta gabato, Ranar Ubangiji ta yi kusa, Rana ce ta gizagizai, Ranar halakar al'ummai.


domin haka, ni Ubangiji Allah na ce, hakika zan saka masa gwargwadon fushinsa, da kishinsa, da ƙiyayyar da ya nuna musu. Zan sanar da kaina a gare su sa'ad da na hukunta shi.


Kamar yadda ya yi farin ciki saboda gādon jama'ar Isra'ila, da ya zama kufai marar amfani, haka nan zan yi da shi, wato Seyir. Zai zama kufai marar amfani, wato Dutsen Seyir da dukan Edom. Sa'an nan mutane za su sani ni ne Ubangiji!”


Taku ta ƙare a wannan rana! Gama ranar Ubangiji ta kusa, Halaka daga wurin Maɗaukaki ta zo.


Ku busa ƙaho, ku yi gangami, A cikin Sihiyona, tsattsarkan dutsen Allah! Duk mutanen ƙasar za su yi rawar jiki, Domin ranar Ubangiji tana zuwa, ta yi kusa.


Ubangiji yakan umarci rundunarsa, Rundunarsa mai cika umarninsa babba ce, mai ƙarfi, Gama ranar Ubangiji babba ce mai banrazana. Wa zai iya daurewa da ita?


Taku ta ƙare, ku da kuke marmarin zuwan ranan nan ta Ubangiji! Wane amfani wannan rana za ta yi muku? Rana ta baƙin ciki ce, Ba ta murna ba.


Ranar Ubangiji za ta kawo baƙin ciki, Ba murna ba. Rana ce ta damuwa ba ta fara'a ba.


Da fushi da hasala zan yi sakayya A kan al'umman da ba su yi biyayya ba.”


Saboda ka washe al'umman duniya da yawa, Sauran mutanen duniya duka za su washe ka, Saboda jinin mutane, da wulakancin da ka yi wa duniya, Da birane, da mazauna a cikinsu.


Don da irin hukuncin da kuka zartar, da shi za a zartar muku. Mudun da kuka auna, da shi za a auna muku.


Gama Shari'a marar jinƙai ce ga wanda ba ya nuna jinƙai. Amma jinƙai yana rinjayar hukunci.


Ya kuma ce, “Sarakuna saba'in waɗanda aka yanyanke manyan yatsotsinsu na hannu da na ƙafa, suka kalaci abincinsu a ƙarƙashin teburina. Allah kuwa ya yi mini kamar yadda na yi musu.” Suka kawo shi Urushalima, a nan ya mutu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan