Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Obadiya 1:10 - Littafi Mai Tsarki

10 “Saboda kama-karyar da ka yi wa Yakubu ɗan'uwanka, Za a sa ka ka sha kunya, Za a hallaka ka har abada.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Saboda halin kama-karyar da kika yi wa ɗan’uwanka Yaƙub, za ki sha kunya; za a hallaka ki har abada.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Obadiya 1:10
30 Iomraidhean Croise  

Amma Yakubu ya ce wa Rifkatu mahaifiyarsa, “Ga shi fa, ɗan'uwana Isuwa gargasa ne, ni kuwa mai sulɓi ne.


Isuwa dai ya ƙi jinin Yakubu saboda albarkar da mahaifinsa ya sa masa. Sai Isuwa ya ce a ransa, “Kwanakin makoki domin mahaifina suna gabatowa, sa'an nan zan kashe Yakubu ɗan'uwana.”


Gama Edomawa suka sāke kai wa Yahuza yaƙi, suka kama mutane suka tafi da su.


Ka sa kunya ta rufe maƙiyana, Ka sa su sa kunyarsu kamar riga.


Zan sa maƙiyansa su sha kunya, Amma mulkinsa zai arzuta. Ya kuma kahu.”


Ka tuna, ya Ubangiji, da abin da Edomawa suka yi, A ranar da aka ci Urushalima. Ka tuna da yadda suka ce, “A ragargaza ta har ƙasa!”


Sabili da kai ne aka ci mutuncina, Kunya ta rufe ni.


Ka sa shi ya tsofe kafin lokacinsa, Ka rufe shi da kunya.


Mutumin kirki yakan karɓi albarka, maganganun mugun kuwa sukan ɓoye mugun halinsa.


Wanda ya yi wa matalauci ba'a, Mahaliccinsa yake yi wa zargi. Idan kana murna da hasarar wani, za a hukunta ka.


Ga abin da Ubangiji ya faɗa a kan mugayen maƙwabtan Isra'ila waɗanda suka taɓa gādon da ya ba jama'arsa Isra'ila su gada. “Saboda haka zan tumɓuke su daga cikin ƙasarsu. Zan kuma tumɓuke mutanen Yahuza daga cikinsu.


Bari mu kwanta mu sha kunyarmu, bari kuma rashin kirkinmu ya rufe mu. Gama mun yi wa Ubangiji Allahnmu zunubi mu da kakanninmu, tun daga ƙuruciyarmu har zuwa yau, ba mu yi biyayya ga maganar Ubangiji Allahnmu ba.”


Gama ni Ubangiji na rantse da zatina, cewa Bozara za ta zama abar tsoro, da abar dariya, da kufai, da abar la'ana. Dukan garuruwanta za su zama kufai har abada.”


Mun sha kunya saboda zargin da ake yi mana, Kunya ta rufe mu, Gama baƙi sun shiga tsarkakan wurare na Haikalin Ubangiji.


Ki yi farin ciki, ki yi murna, ke Edom, Wadda kike zaune cikin ƙasar Uz. Amma fa za a ba ki ƙoƙo ki sha, Ki bugu har ki yi tsiraici.


Ya Sihiyona, hukunci a kan muguntarki ya ƙare, Ba zai ƙara barinki a ƙasar bauta ba. Amma zai hukunta ki saboda muguntarki, ya Edom, Zai tone zunubanki.


Zan maishe shi kufai marar amfani har abada. Ba wanda zai zauna a cikin biranensa. Sa'an nan zai sani ni ne Ubangiji.


Sun sa tufafin makoki, razana ta kama su, fuskokinsu kuma suna cike da kunya, akwai sanƙo a kawunansu.


“Masar za ta zama hamada, Edom kuma za ta zama kufai, Saboda kama-karya da suka yi wa mutanen Yahuza, Saboda sun zubar da jinin marasa laifi a ƙasarsu,


Ubangiji ya ce, “Mutanen Edom sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, Don sun farauci 'yan'uwansu, Isra'ilawa, Suka ƙi su nuna musu jinƙai. Ba su yarda su huce daga fushinsu ba.


Sa'an nan maƙiyina wanda suke ce mini, “Ina Ubangiji Allahnka?” Zai gani, ya kuma ji kunya. Idanuna za su gan shi lokacin da aka tattake shi Kamar taɓo a titi.


“Kada ku ji ƙyamar Ba'edome gama shi danginku ne. Kada kuma ku ji ƙyamar Bamasare don kun yi baƙunci a ƙasarsa.


'Ya'yansu tsara ta uku, za su iya shiga taron jama'ar Ubangiji.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan