Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Obadiya 1:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Annabcin Obadiya ke nan. Wannan shi ne abin da Ubangiji Allah ya ce a kan al'ummar Edom. Ubangiji ya aiki manzonsa wurin sauran al'umma, Mun kuwa ji saƙonsa cewa, “Ku zo! Mu tafi mu yi yaƙi da Edom!”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Wahayin Obadiya. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce a kan Edom. Mun ji saƙo daga wurin Ubangiji cewa, An aiki jakada zuwa ga al’ummai yă faɗa musu cewa, “Ku tashi, mu tafi mu yi yaƙi da ita.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Obadiya 1:1
28 Iomraidhean Croise  

Sai Isuwa ya ce wa Yakubu, “Ka ɗibar mini jan fatenka in sha, gama ina fama da yunwa!” Saboda haka aka kira sunansa Edom.


Saboda haka Isuwa ya zauna a ƙasar Seyir ta tuddai. Isuwa shi ne Edom.


Waɗannan su ne zuriyar Isuwa, kakan Edomawa, a ƙasar Seyir ta tuddai.


Ka tuna, ya Ubangiji, da abin da Edomawa suka yi, A ranar da aka ci Urushalima. Ka tuna da yadda suka ce, “A ragargaza ta har ƙasa!”


Wannan shi ne jawabi a kan Edom. Wani daga Edom ya kira ni ya ce, “Ya mai tsaro, gari ya kusa wayewa? Ka gaya mini har sai yaushe zai waye?”


Sai na amsa na ce, “Gari zai waye, amma za a sāke yin dare! Idan kana so ka sāke yin tambaya, sai ka sāke zuwa, ka tambaya.”


Ko da yake jakadunsu sun riga sun isa Zowan da Hanes, biranen Masar,


Sai na karɓi ƙoƙon daga wurin Ubangiji, na sa dukan al'umman da Ubangiji ya aike ni gare su, su sha daga cikinsa.


Kada zuciyarku ta yi suwu, Kada kuma ku ji tsoro saboda labarin da ake ji a ƙasar, Labari na wannan shekara dabam, na wancan kuma dabam, A kan hargitsin da yake a ƙasar, Mai mulki ya tasar wa mai mulki.


Ubangiji ya kuma yi magana da ni, ya ce,


“Masar za ta zama hamada, Edom kuma za ta zama kufai, Saboda kama-karya da suka yi wa mutanen Yahuza, Saboda sun zubar da jinin marasa laifi a ƙasarsu,


“Wanda zai huda garu, shi zai yi musu jagora, Za su fita ƙofar, su wuce, su fice ta cikinta. Sarkinsu zai wuce gabansu, Ubangiji kuma yana kan gaba.”


Za ku kuma riƙa jin labarin yaƙe-yaƙe da jitajitarsu. Kada fa hankalinku ya tashi, don lalle ne a yi haka, amma ƙarshen tukuna.


In kuma kun jin labarin yaƙe-yaƙe da jita-jitarsu, kada hankalinku ya tashi. Lalle ne wannan ya auku, amma ƙarshen tukuna.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan