Nehemiya 8:3 - Littafi Mai Tsarki3 Ya karanta Littafin, yana fuskantar filin Ƙofar Ruwa, a gaban mata da maza, da waɗanda za su iya fahimta. Mutane duka kuwa suka kasa kunne ga karatun Attaura, tun da sassafe har zuwa rana tsaka. Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 20203 Ya karanta Dokar da ƙarfi daga safe har tsakar rana yayinda yake a kan dandali da yake fuskantar dandali a gaban Ƙofar Ruwa, gaban maza, mata da kuma sauran mutanen da za su iya fahimta. Dukan mutane kuwa suka saurara a hankali ga karatun Littafin Dokar. Faic an caibideil |
Sai Ezra, magatakarda, ya tsaya a wani dakali na itace, wanda suka shirya musamman domin wannan hidima. Sai Mattitiya, da Shema, da Anaya, da Uriya, da Hilkaya, da Ma'aseya, suka tsaya a wajen damansa, a wajen hagunsa kuwa Fedaiya, da Mishayel, da Malkiya, da Hashum, da Hashbaddana, da Zakariya, da Meshullam suka tsaya.