Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Nehemiya 8:2 - Littafi Mai Tsarki

2 A ran ɗaya ga watan bakwai, sai Ezra, firist, ya kawo Attaura a gaban taron jama'a, mata da maza, da dukan waɗanda za su ji, su fahimta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Saboda haka a rana ta farko ga watan bakwai, Ezra firist, ya kawo Doka a gaban taro, wanda ya ƙunshi maza da mata da dukan waɗanda za su iya fahimta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Nehemiya 8:2
14 Iomraidhean Croise  

suka haɗa kai da 'yan'uwansu, da shugabanninsu, suka rantse, cewa la'ana ta same su idan ba su kiyaye dokokin Allah waɗanda ya ba bawansa Musa ba. Suka rantse za su kiyaye, su aikata umarnai, da ka'idodi, da dokokin Ubangijinmu.


A wannan rana aka karanta daga littafin Musa a kunnuwan jama'a. A cikinsa aka tarar da inda aka rubuta, cewa kada Ba'ammone, ko mutumin Mowab ya shiga taron jama'ar Allah.


Kowace rana, tun daga rana ta fari zuwa rana ta ƙarshe, Ezra yakan karanta musu daga cikin littafin dokokin Allah. Suka kiyaye idin har kwana bakwai. A rana ta takwas kuma suka muhimmin taro bisa ga ka'ida.


Nehemiya kuwa wanda yake mai mulki, da Ezra, firist da magatakarda, da Lawiyawa waɗanda suka fassara wa jama'a dokokin, suka ce wa dukan jama'a, “Wannan rana tsattsarka ce, ta Ubangiji Allahnku, kada ku yi baƙin ciki ko kuka.” Gama mutane duka sai kuka suke sa'ad da aka karanta musu dokokin.


A rana ta ashirin da huɗu ga watan nan, sai jama'ar Isra'ila suka taru, suna azumi, suna saye da tufafin makoki, suna zuba toka a kansu.


Suna gunaguni a kaina suna cewa, “Su wa wannan mutum yake tsammani yana koya musu? Wa yake bukatar jawabinsa? Sai ga 'yan yaran da aka yaye kaɗai yake da amfani!


ya ce wa Isra'ilawa su mai da rana ta fari ga wata na bakwai ta zama ranar hutu musamman, sa'ad da za su ji busar ƙaho, sai su taru domin yin sujada.


Gama ya kamata bakin firist ya kiyaye ilimi, wajibi ne firistoci su koyar da ilimin gaskiya na Allah, a gare su mutane za su tafi su koyi nufina, domin su manzannina ne, ni Ubangiji Mai Runduna.


A rana ta fari ga wata na bakwai za a taru domin yin sujada, ba za a yi aiki a ranar ba. A ranar za a busa ƙahoni.


Domin tun zamanin dā, a kowane gari akwai masu yin wa'azi da littattafan Musa, ana kuma karanta su a majami'u kowace Asabar.”


Sa'ad da ya hau gadon sarautar, sai ya sa a rubuta masa dokoki daga cikin littafin dokoki wanda yake wurin Lawiyawan da suke firistoci.


Babu wata kalmar da Musa ya umarta, da Joshuwa bai karanta a gaban dukan taron Isra'ilawa ba, tare da mata da ƙanana, da baƙin da suke zaune tare da su.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan