Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Nehemiya 8:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Dukan jama'a suka taru wuri ɗaya a filin Ƙofar Ruwa, suka faɗa wa Ezra, magatakarda, ya kawo Attaura ta Musa wanda Ubangiji ya ba Isra'ilawa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 sai dukan mutane suka taru kamar mutum guda a dandali a gaban Ƙofar Ruwa. Suka faɗa wa Ezra malamin Doka yă fitar da Littafin Dokar Musa, wanda Ubangiji ya umarta domin Isra’ila.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Nehemiya 8:1
25 Iomraidhean Croise  

Ezra ɗin ya taho daga Babila. Shi malami ne, masanin shari'ar Musa, wadda Ubangiji Allah na Isra'ila ya bayar. Sarki kuwa ya ba shi dukan abin da ya roƙa, gama Ubangiji Allahnsa yana tare da shi.


Ma'aikatan Haikali da suke zaune a Ofel suka yi gyare-gyare zuwa wani wuri daura da Ƙofar Ruwa wajen gabas, har zuwa wata doguwar hasumiya.


Sai Hilkiya ya ce wa magatakarda Shafan, “Na gāno Littafin Shari'a a Haikalin Ubangiji.” Sai Hilkiya ya ba Shafan littafin.


Wannan ita ce takardar doka da sarki Artashate ya ba Ezra, wanda yake firist da magatakarda, ƙwararre cikin sha'anin dokoki da umarnan Ubangiji a cikin Isra'ilawa.


Saboda haka nake aiko muku da annabawa, da masu hikima, da masanan Attaura, za ku kashe waɗansunsu, ku gicciye waɗansu, ku kuma yi wa waɗansu bulala a majami'unku, kuna binsu gari gari kuna gwada musu azaba.


“Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kun toshe wa mutane ƙofar Mulkin Sama. Ku kanku ba ku shiga ba, kuna kuwa hana masu niyyar shiga shiga.


“Malaman Attaura da Farisiyawa suka tsaya a matsayin Musa.


Sai ya ce musu, “To, duk malamin Attaura da ya zama almajirin Mulkin Sama, kamar maigida yake, wanda ya ɗebo dukiya sabuwa da tsohuwa daga taskarsa.”


“Ku tuna da koyarwar bawana Musa, da dokoki, da umarnai waɗanda na ba shi a kan Dutsen Horeb, domin dukan jama'ar Isra'ila su kiyaye.


Ga amsar da za ku ba su, ku ce, “Ku kasa kunne ga koyarwar Ubangiji. Kada ku kasa kunne ga 'yan bori. Gama abin da suka faɗa muku ba zai amfane ku ba.”


A Ƙofar Maɓuɓɓuga kuwa, sai suka yi gaba sosai wajen matakan birnin Dawuda, wajen hawan garu, daga bisa gidan Dawuda, zuwa Ƙofar Ruwa wajen gabas.


Sai suka tafi suka kawo rassan, suka yi wa kansu bukkoki a kan rufin sorayensu, da a dandalinsu, da cikin harabar Haikalin Allah, da a dandalin Ƙofar Ruwa, da a dandalin Ƙofar Ifraimu.


Dukan jama'a kuwa suka tashi gaba ɗaya, suna cewa, “Daga cikinmu ba wanda zai koma alfarwarsa ko kuwa gidansa.


Dukan jama'ar Isra'ila fa suka fito tun daga Dan a arewa har zuwa Biyer-sheba a kudu da kuma Gileyad daga gabas. Suka hallara gaba ɗaya a gaban Ubangiji a Mizfa.


Sai sarki ya haura zuwa Haikalin Ubangiji tare da dukan mutanen Yahuza, da mazaunan Urushalima, da firistoci, da Lawiyawa, da dukan jama'a, babba da yaro. Sai ya karanta dukan maganar da take a littafin alkawari wanda aka gāno a Haikalin Ubangiji, a kunnen dukansu.


Gama Ezra ya ba da kansa ga yin nazarin dokokin Allah, ya kiyaye su, ya kuma koyar wa Isra'ilawa dokoki da farillan Allah.


Ya karanta Littafin, yana fuskantar filin Ƙofar Ruwa, a gaban mata da maza, da waɗanda za su iya fahimta. Mutane duka kuwa suka kasa kunne ga karatun Attaura, tun da sassafe har zuwa rana tsaka.


Sai suka kawo abin da Musa ya umarce su a gaban alfarwa ta sujada. Dukan taron jama'a suka matso kusa, suka tsaya a gaban Ubangiji.


sa'ad da dukan Isra'ilawa za su hallara a gaban Ubangiji Allahnku a inda zai zaɓa, to, sai ku karanta musu waɗannan dokoki su ji da kunnuwansu.


Sa'an nan ya haura zuwa Haikalin Ubangiji tare da dukan jama'ar Yahuza, da dukan mazaunan Urushalima, da firistoci, da annabawa, da jama'a duka, ƙanana da manya. Sai ya karanta musu dukan maganar littafin alkawarin da aka iske a Haikalin Ubangiji.


Bayan wannan a zamanin Artashate Sarkin Farisa, sai Ezra ya gane da asalinsa, wato shi na ɗan Seraiya, da Azariya, da Hilkiya,


Waɗannan suna nan a zamanin Yoyakim ɗan Yeshuwa, jikan Yehozadak, da zamanin mai mulki Nehemiya, da Ezra, firist da magatakarda.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan