Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Nehemiya 7:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Sa'an nan na ce musu, kada su buɗe ƙofofin Urushalima da sassafe, sai rana ta cira sosai, su kuma kulle ƙofofin da ƙarfe kafin matsara su tashi wajen faɗuwar rana. Su samo matsara daga mazaunan Urushalima, su sa su tsaye a muhimman wurare, waɗansunsu kuma suna zaga gidaje.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Na ce musu, “Kada a buɗe ƙofofin Urushalima da sassafe sai rana ta fito sosai. Yayinda matsaran ƙofofi suna aiki, a kulle ƙofofin a sa musu sakata kafin matsaran su tashi, wajen fāɗuwar rana. Ku kuma naɗa mazaunan Urushalima a matsayin masu tsaro, waɗansunsu a wuraren aiki, waɗansun kuma kusa da gidajensu.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Nehemiya 7:3
8 Iomraidhean Croise  

Magariba na yi kafin ranar Asabar, sai na yi umarni a rufe ƙofofin Urushalima, kada a buɗe su sai Asabar ta wuce. Na sa waɗansu barorina a ƙofofin, don kada su bari a shigo da kaya ran Asabar.


Bayansu kuma Biliyaminu da Hasshub suka yi gyara daura da gidansu. Bayansu kuma Azariya, ɗan Ma'aseya, wato jikan Ananiya, ya yi gyara kusa da gidansa.


sai na ba ɗan'uwana, Hanani, da Hananiya, shugaban kagara, aikin riƙon Urushalima. Shi Hananiya mai aminci ne, mai tsoron Allah, fiye da sauran mutane.


Birnin yana da faɗi da girma, amma mutanen da suke ciki kaɗan ne, ba a kuma gina gidaje ba tukuna.


Idan ba Ubangiji ne ya gina gidan ba, Aikin magina banza ne. Idan ba Ubangiji ne ya tsare birnin ba, Ba wani amfani a sa matsara su yi tsaro.


Shi yake riƙe da ƙofofinki da ƙarfi, Yakan sa wa jama'arki albarka.


“Ga shi, na aike ku kamar tumaki a tsakiyar kyarketai. Don haka sai ku zama masu azanci kamar macizai, da kuma marasa ɓarna kamar kurciyoyi.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan