Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Nehemiya 7:2 - Littafi Mai Tsarki

2 sai na ba ɗan'uwana, Hanani, da Hananiya, shugaban kagara, aikin riƙon Urushalima. Shi Hananiya mai aminci ne, mai tsoron Allah, fiye da sauran mutane.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Na sa ɗan’uwana Hanani tare da Hananiya shugaban fada aikin riƙon Urushalima, domin shi Hananiya mutum mai mutunci ne, mai tsoron Allah fiye da yawancin mutane.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Nehemiya 7:2
21 Iomraidhean Croise  

A kan rana ta uku, Yusufu ya ce musu, “Abin da za ku yi in bar ku da rai ke nan, gama ina tsoron Allah,


Allah na Isra'ila ya yi magana, Matsaron Isra'ila ya ce mini, ‘Sarkin da yake mulkin mutane da adalci, Wanda yake mulki da tsoron Allah,


Rabuwata da kai ke da wuya, sai Ruhun Ubangiji ya kai ka wurin da ban sani ba, don haka, in na tafi na faɗa wa Ahab, in bai same ka ba, to, ni zai kashe, ko da yake ni baranka, tun ina saurayi nake tsoron Ubangiji.


Ahab kuwa ya kira Obadiya, shugaban gidansa. Obadiya kuwa mai tsoron Ubangiji ne sosai.


sai Hanani, ɗaya daga cikin 'yan'uwana, ya zo tare da waɗansu mutanen Yahuza. Na kuwa tambaye shi labarin Yahudawan da suka tsira, suka koma daga zaman talala, da labarin Urushalima.


Sai na sa Shelemiya, firist, da Zadok, magatakarda, da Fedaiya daga cikin Lawiyawa su zama masu lura da ɗakunan ajiya. Na kuma sa Hanan ɗan Zakkur, jikan Mattaniya ya yi aiki tare da su, gama su amintattu ne. Aikinsu shi ne su raba wa 'yan'uwansu abin da aka kawo.


A kuma ba ni takarda zuwa ga Asaf, sarkin daji, domin ya ba ni katakan da zan yi jigajigan ƙofofin kagarar Haikali, da na garun birnin, da na gidan da zan zauna.” Sarki kuwa ya ba ni abin da na roƙa, gama Allah yana tare da ni.


Waɗanda suka riga ni mulki sun nawaita wa mutane. Sun yi ta karɓar abinci da ruwan inabi daga gare su, banda shekel arba'in kowace rana domin abinci da ruwan inabi. Har ma barorin masu mulki sun nawaya wa mutane. Amma ni ban yi haka ba, saboda ina tsoron Allah.


Sa'an nan na ce musu, kada su buɗe ƙofofin Urushalima da sassafe, sai rana ta cira sosai, su kuma kulle ƙofofin da ƙarfe kafin matsara su tashi wajen faɗuwar rana. Su samo matsara daga mazaunan Urushalima, su sa su tsaye a muhimman wurare, waɗansunsu kuma suna zaga gidaje.


Akwai wani mutum a ƙasar Uz, mai suna Ayuba, amintacce ne, mai tsoron Allah. Shi mutumin kirki ne, natsattse, yana ƙin aikata kowace irin mugunta.


Zan yarda da waɗanda suke amincewa da Allah, Zan yardar musu si yi zamansu a fādata, Zan yarda wa waɗanda suke da tabbataccen aminci Su yi mini hidima.


Ka kuma zaɓa daga cikin jama'a isassun mutane, masu tsoron Allah, amintattu, waɗanda suke ƙyamar cin hanci. Ka naɗa su shugabannin jama'a na dubu dubu da na ɗari ɗari, da na hamsin hamsin, da na goma goma.


Sai shugabannin, da su muƙaddasan suka nemi Daniyel da laifi game da ayyukan mulki, amma ba su sami laifin da za su tuhume shi da shi ba, domin shi amintacce ne, ba shi da kuskure ko ha'inci.


Ba haka nake magana da bawana Musa ba, na sa shi ya lura da dukkan jama'ata Isra'ila.


“Wane ne amintaccen bawan nan mai hikima, da ubangidansa ya ba shi riƙon gidansa, yă riƙa ba su abincinsu a kan kari?


Sai ubangijinsa ya ce masa, ‘Madalla, bawan kirki, mai aminci. Kā yi gaskiya a kan ƙaramin abu, zan ɗora ka a kan mai yawa. Ka zo ku yi farin ciki tare da ubangidanka.’


Har wa yau dai, abin da ake bukata ga mai riƙon amana, a same shi amintacce.


Abin da ka ji a guna a gaban shaidu masu yawa kuwa, sai ka danƙa wa amintattun mutane, waɗanda su ma za su koya wa waɗansu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan