Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Nehemiya 5:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Akwai waɗanda suka ce, “Mu da 'ya'yanmu mata da maza muna da yawa, sai mu sami hatsi don mu ci mu rayu.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Waɗansu suka ce, “Mu da ’ya’yanmu maza da mata muna da yawa, muna bukatar hatsi domin mu ci mu rayu.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Nehemiya 5:2
11 Iomraidhean Croise  

Duniya duka kuwa ta zo Masar wurin Yusufu, ta sayi hatsi saboda yunwa ta tsananta a duniya duka.


Ga shi kuwa, na ji akwai hatsi a Masar, ku gangara ku sayo mana hatsi a can domin mu rayu, kada mu mutu.”


Sai Yahuza ya ce wa Isra'ila, mahaifinsu, “Ka sa saurayin a hannuna, mu tashi mu tafi, mu sami abinci mu rayu, kada mu mutu, da mu da kai da ƙanananmu.


Kada ka bar mu mu mutu, ka yi wata dabara! Kada ka bari mu rasa gonakinmu. Ka musaye mu da abinci, mu da gonakunmu. Mu kuwa za mu zama bayin Fir'auna, ka kuma ba mu iri domin mu rayu, kada mu mutu don kuma kada ƙasar ta zama kango.”


Matar wani daga cikin ƙungiyar annabawa da ya rasu, ta kai kuka wurin Elisha, ta ce, “Maigidana, baranka, wato mijina, ya rasu, ka kuwa sani shi mai tsoron Ubangiji ne, amma wanda yake binsa bashi ya zo zai kwashe 'ya'yana biyu su zama bayinsa.”


Waɗansu kuma suka ce, “Saboda yunwa mun jinginar da gonakinmu, da gonakin inabinmu, da gidajenmu don mu sami hatsi.”


Kun yi shuka da yawa, kun girbe kaɗan. Kun ci, amma ba ku ƙoshi ba. Kun sha ruwa, amma bai kashe muku ƙishi ba. Kun sa tufafi, amma ba wanda ya ji ɗumi. Wanda yake karɓar albashi kuwa, sai ka ce yana sawa a huɗajjen aljihu.”


Idan ba za ku kasa kunne ba, idan ba za ku sa a zuciyarku ku girmama sunana ba, to, zan aukar muku da la'ana, zan la'antar da albarkunku. Koyanzu ma na riga na la'antar da su domin ba ku riƙe umarnina a zuciyarku ba, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.


“Kada ku ba danginku rance da ruwa, ko rancen kuɗi ne, ko na abinci, ko na kowane irin abu da akan ba da shi da ruwa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan