Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Nehemiya 4:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Sa'ad da Sanballat ya ji muna ginin garun, sai ya husata ƙwarai, ya yi wa Yahudawa ba'a.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Da Sanballat ya ji cewa muna sāke ginin katangar, sai ya husata, ya haukace ƙwarai. Ya yi wa Yahudawa dariya,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Nehemiya 4:1
13 Iomraidhean Croise  

Ɗaya daga cikin 'ya'yan Yoyada ɗan Eliyashib, babban firist, surukin Sanballat ne, Bahorone, saboda haka sai na kore shi daga wurina.


Amma Sanballat Bahorone, da Tobiya, Ba'ammone, bawa, ba su ji daɗi ba ko kaɗan sa'ad da suka ji labari, cewa wani ya zo domin ya inganta zaman lafiyar mutanen Isra'ila.


Amma sa'ad da Sanballat Bahorone, da Tobiya Ba'ammone, bawa, da Geshem Balarabe, suka ji labari, sai suka yi mana ba'a, suka raina mu, suka ce, “Me kuke yi? Kuna yi wa sarki tayarwa ne?”


A cikin kwana hamsin da biyu aka gama garun, ran ashirin da biyar ga watan Elul.


Sa'ad da abokan gābanmu da dukan al'umman da suke kewaye da mu suka ji, sai suka ji tsoro, gabansu kuma ya faɗi, gama sun gane, da taimakon Allahnmu muka yi wannan aiki.


Sarki Zadakiya ya ce wa Irmiya, “Ina jin tsoron Yahudawa waɗanda suka gudu zuwa wurin Kaldiyawa. Kila a bashe ni a hannunsu, su ci mutuncina.”


Da Hirudus ya ga masanan nan sun mai da shi wawa, sai ya hasala ƙwarai, ya aika a karkashe dukan 'yan yara maza da suke Baitalami da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa ƙasa, gwargwadon lokacin da ya tabbatar a gun masanan nan.


Suka yi wani rawani na ƙaya, suka sa masa a kā, suka danƙa masa sanda a hannunsa na dama, suka kuma durƙusa a gabansa, suna yi masa ba'a suna cewa, “Ranka ya daɗe, Sarkin Yahudawa!”


Amma babban firist ya taso, da duk waɗanda suke tare da shi, wato 'yan ɗariƙa Sadukiyawa, suna kishi gaya,


Har wa yau kuma, waɗansu suka sha ba'a da bulala, har ma da ɗauri da jefawa a cikin kurkuku.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan