Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Nehemiya 3:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Kusa da Zadok kuwa mutanen Tekowa suka yi nasu gyare-gyare, amma manyansu ba su sa hannu ga aikin shugabanninsu ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Mutanen Tekowa ne suka yi gyare-gyare biye da shi, amma manyan garinsu suka ƙi su sa hannu cikin aikin da shugabanninsu suka bayar.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Nehemiya 3:5
17 Iomraidhean Croise  

sai ya aika zuwa Tekowa a kira masa wata mace mai hikima. Da ta zo, ya ce mata, “Ki yi kamar kina makoki, ki sa rigunan makoki, kada ki shafa mai. Ki yi kamar wadda ta yi kwanaki da yawa tana makokin rasuwar wani.


Ya gina Baitalami, da Itam, da Tekowa,


Bayansu kuma mutanen Tekowa suka gyara wani sashi daura da babbar doguwar hasumiya, har zuwa garun Ofel.


Kusa da su kuma, sai Meremot ɗan Uriya, wato jīkan Hakkoz ya yi gyare-gyare. Kusa da shi kuma sai Meshullam ɗan Berikiya jikan Meshezabel ya yi gyare-gyare. Kusa da shi kuma sai Zadok ɗan Ba'ana ya yi gyare-gyare.


Yoyada ɗan Faseya, da Meshullam ɗan Besodeya, suka gyara Tsohuwar Ƙofa, suka kafa katakanta, suka sa ƙyamarenta, da sandunan ƙarfe na kulle ƙofofinta.


Sai na faɗa wa Zadakiya Sarkin Yahuza wannan magana cewa, “Ka ɗaura karkiyar Sarkin Babila a wuyanka, ka bauta masa, shi da mutanensa, don ka rayu!


Ya ce ya yi wa kansa karkiyar itace da maɗaurai na fata ya ɗaura su a wuyansa,


“ ‘Amma idan wata al'umma ko wani mulki bai yarda ya bauta wa Nebukadnezzar, Sarkin Babila ba, bai kuma ɗaura karkiyar Sarkin Babila a wuyansa ba, zan hukunta wa wannan al'umma da takobi, da yunwa, da annoba, har in hallaka ta, ta hannun Nebukadnezzar, ni Ubangiji na faɗa.


“Ya ku mutanen Biliyaminu, ku gudu neman mafaka, Daga cikin Urushalima! Ku busa ƙaho a Tekowa, Ku ba da alama a Bet-akkerem, Gama masifa da babbar halaka sun fito daga arewa.


Ga zantuttukan Amos, ɗaya daga cikin makiyayan ƙauyen Tekowa. Allah ya bayyana wa Amos wannan saƙo, tun shekara biyu kafin girgizar duniya, a lokacin da Azariya yake sarautar Yahuza, Yerobowam ɗan Yehowash kuwa yake sarautar Isra'ila.


Ku shiga bautata, ku kuma koya a gare ni, domin ni mai tawali'u ne, marar girmankai, za ku kuwa sami kwanciyar rai.


Saboda haka, don me kuke gwada Allah, ta ɗora wa almajiran nan kayan da mu, duk da kakanninmu, muka kasa ɗauka?


Ku dubi kiranku da aka yi, ya ku 'yan'uwa, a cikinku, ai, ba a kira masu hikima irin ta duniya da yawa ba, masu iko kuma ba su da yawa, haka ma masu asali ma ba yawa.


Mala'ikan Ubangiji ya ce, “Ka la'anta Meroz, Ka la'anta mazauna cikinta sosai, Gama ba su kawo wa Ubangiji gudunmawa ba, Su zo su yi yaƙi kamar sojoji dominsa.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan