Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Nehemiya 3:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Eliyashib, babban firist kuwa, tare da 'yan'uwansa firistoci, suka tashi suka gina Ƙofar Tumaki. Suka tsarkake ta, suka sa mata ƙyamarenta. Suka tsarkake garun zuwa Hasumiyar Ɗari da Hasumiyar Hananel.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Eliyashib babban firist da ’yan’uwansa firistoci suka tashi suka sāke gina Ƙofar Tumaki. Suka tsarkake ta, suka sa ƙofofinta a wurarensu, suka yi ginin har Hasumiyar Ɗari, wadda suka tsarkake, da kuma Hasumiyar Hananel.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Nehemiya 3:1
19 Iomraidhean Croise  

Yeshuwa shi ne ya haifi Yoyakim, Yoyakim ya haifi Eliyashib, Eliyashib ya haifi Yoyada.


Sai firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu, suka kuma tsarkake jama'a, da ƙofofi, da garun.


da Kuma sama da Ƙofar, Ifraimu da wajen Tsohuwar Ƙofar, da wajen Ƙofar Kifi, da Hasumiyar Hananel, da Hasumiyar Ɗari zuwa Ƙofar Tumaki, sai suka tsaya a Ƙofar Tsaro.


Ɗaya daga cikin 'ya'yan Yoyada ɗan Eliyashib, babban firist, surukin Sanballat ne, Bahorone, saboda haka sai na kore shi daga wurina.


Kafin wannan lokaci Eliyashib, firist, wanda aka sa shi shugaban ɗakunan ajiya na Haikalin Allahnmu, wanda yake da dangantaka da Tobiya,


Bayansa kuma, Baruk ɗan Zabbai, ya gyara wani sashi daga wajen kusurwar, har ya zuwa ƙofar gidan Eliyashib babban firist.


Bayansa kuma Meremot ɗan Uriya, ɗan Hakkoz, ya gyara wani sashi daga ƙofar gidan Eliyashib, zuwa ƙarshen gidan.


Maƙeran zinariya da 'yan kasuwa suka gyara wani sashi tsakanin soron bene daga kusurwa da Ƙofar Tumaki.


Sa'ad da fa aka sanar da Sanballat, da Tobiya, da Geshem Balarabe, da sauran abokan gābanmu, cewa na gina garun, har ba sauran tsaguwa da ta ragu, ko da yake a lokacin ban riga na sa wa ƙofofi ƙyamare ba,


Sa'ad da aka gina garun, aka sa ƙofofinsa, aka kuma sa matsaran ƙofofi, da mawaƙa, da Lawiyawa,


Ina yabonka, ya Ubangiji saboda ka cece ni, Ka kuwa hana magabtana su haɗiye ni.


Ku tafi ku kewaye Dutsen Sihiyona, Ku ƙirga yawan hasumiyarsa.


A cikin dukan abin da kake yi, ka tuna da Ubangiji, shi kuma zai nuna maka hanyar da take daidai.


Ka girmama Ubangiji ta wurin miƙa masa hadaya daga mafi kyau na amfanin gonarka.


“Ga shi, kwanaki suna zuwa da za a sāke gina birnin domin Ubangiji, ni Ubangiji na faɗa, tun daga hasumiyar Hananel zuwa yamma, har zuwa Ƙofar Kan Kusurwa.


Sai ka sani, ka kuma gane, daga lokacin da aka umarta a sāke gina Urushalima har zuwa lokacin da shugaba, Masiha, zai zo, za a yi shekara arba'in da tara, da shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu. Za a sāke gina ta a yi mata tituna da kagara.


Ƙasa dukka za ta zama fili, daga Geba zuwa Rimmon a kudancin Urushalima. Amma Urushalima za ta kasance a kan tudu, za ta miƙe daga Ƙofar Biliyaminu, zuwa wurin da ƙofa ta fari take a dā, har zuwa Ƙofar Kusurwa, sa'an nan ta miƙe daga Hasumiyar Hananel zuwa wuraren matsewar ruwan inabin sarki.


A Urushalima, kusa da Ƙofar Tumaki, akwai wani ruwa da ake ce da shi Betasda da Yahudanci, an kuwa kewaye shi da shirayi biyar.


“Sa'an nan shugabanni za su yi magana da jama'a, su ce, ‘Ko akwai wani mutum a nan wanda ya gina gidan da bai buɗe shi ba tukuna? Sai ya koma gidansa, kada ya mutu a yaƙi, wani dabam ya yi bikin buɗewar.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan