Aka faɗa wa Dawuda cewa, “Ahitofel yana cikin 'yan maƙarƙashiya tare da Absalom.” Sai Dawuda ya yi addu'a, ya ce, “Ya Ubangiji, ina roƙonka, ka wofintar da shawarar Ahitofel.”
Ya Ubangiji, ka kasa kunne ga addu'ar bawanka, da addu'o'in bayinka, waɗanda suke jin daɗin girmama sunanka. Ka ba bawanka nasara yau ka sa ya sami tagomashi a gaban mutumin nan.”
Na ce, “Ya Ubangiji Allah na Sama, Allah mai girma, mai banrazana, mai cika alkawari, mai nuna madawwamiyar ƙauna ga waɗanda suke ƙaunarka, wato masu kiyaye umarnanka,
Ni kuwa sai na amsa musu, na ce, “Allah na Sama zai ba mu nasara, saboda haka mu mutanensa za mu tashe, mu kama gini, amma ba ruwanku, ba hakkinku, ba ku da wani abin tunawa a Urushalima.”
sa'an nan na ce wa sarki, “Idan ka yarda, idan kuma na sami tagomashi a wurinka, ya sarki, ka yardar mini in tafi Yahuza, birnin kakannina, inda makabartarsu take domin in sāke gina shi.”
A rana ta biyu, sa'ad da suke shan ruwan inabi, sai sarki ya sāke ce wa Esta, “Mece ce bukatarki, sarauniya Esta? Za a yi miki. Mene ne roƙonki? Za a ba ki, ko da rabin mulkina ne.”