Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Nehemiya 2:3 - Littafi Mai Tsarki

3 na ce wa sarki, “Ranka ya daɗe, me zai hana fuskata ta ɓaci, da yake birni inda makabartar kakannina take ya zama kango, an kuma ƙone ƙofofinsa da wuta?”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 na amsa na ce wa sarki, “Ran sarki yă daɗe! Me zai hana fuskata ta ɓaci, sa’ad da birnin da aka binne kakannina tana zaman kango, aka kuma rushe ƙofofinsa da wuta?”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Nehemiya 2:3
21 Iomraidhean Croise  

Bat-sheba kuwa ta rusuna har ƙasa, domin girmamawa, ta ce, “Ran ubangijina sarki ya daɗe har abada!”


A shekara ta goma sha tara ta sarautar Nebukadnezzar Sarkin Babila, a rana ta bakwai ga watan biyar, sai Nebuzaradan, mashawarcin sarki, shugaban sojojinsa kuma, ya shiga Urushalima.


Yana da shekara talatin da biyu, ya ci sarauta, ya yi shekara takwas yana mulki a Urushalima, ba wanda ya yi baƙin cikin mutuwarsa. Aka binne shi a birnin Dawuda, amma ba a kaburburan sarakuna ba.


Ahaz ya rasu, suka binne shi cikin birnin Urushalima, amma ba su kai shi hurumin sarakunan Isra'ila ba. Hezekiya ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.


Sai Hezekiya ya rasu, suka binne shi a sashe na bisa na hurumin 'ya'yan Dawuda, maza. Dukan Yahuza da mazaunan Urushalima suka girmama shi sa'ad da ya rasu. Sai Manassa ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.


Suka ƙone Haikalin Allah suke rushe garun Urushalima, suka ƙone dukan fādodinta, suka lalatar da dukan kayanta masu daraja.


Sai suka ce mini, “Waɗanda suka tsira, suka koma daga zaman talala, da suke can lardin, suna cikin wahala ƙwarai, suna kuma shan kunya. Garun Urushalima kuma ya rushe, ƙofofi sun ƙone.”


Da na fita, sai na bi ta Ƙofar Kwari zuwa Rijiyar Dila da Ƙofar Juji, na dudduba garun Urushalima, wanda aka rushe, da ƙofofinsa da wuta ta cinye.


Gama ƙaƙa zan iya daurewa da ganin masifa da hallaka na mutanena da dangina?”


Bayinka suna ƙaunarta, Ko da yake an hallakar da ita, Suna jin tausayinta, Ko da yake ta zama kufai.


Sauran al'umma za su ji tsoron Ubangiji, Dukan sarakunan duniya za su ji tsoron ikonsa.


Da ma kada in ƙara iya raira waƙa, Idan na manta da ke, Idan ban tuna ke ce Babbar abar farin ciki ba!


Ina fama da zazzaɓi, Ina rashin lafiya ƙwarai.


A kan rana ta goma ga watan biyar a shekara ta goma sha tara ta sarautar Nebukadnezzar, Sarkin Babila, sai Nebuzaradan shugaban matsara da kuma ɗan majalisar sarki, ya zo Urushalima.


Ƙofofinta sun nutse ƙasa, Ya lalatar, ya kakkarya ƙyamarenta, An kai sarkinta da mahukuntanta cikin al'ummai, Inda ba a bin dokokin annabawanta, Ba su kuma samun wahayi daga wurin Ubangiji.


Sai Kaldiyawa suka yi magana da sarki da Aramiyanci, suka ce, “Ran sarki ya daɗe! Ka faɗa wa barorinka mafarkin, za mu kuwa yi maka fassararsa.”


Suka ce wa sarki Nebukadnezzar, “Ranka ya daɗe.


Da sarauniya ta ji maganganun sarki da na manyan fādawansa, sai ta shiga babban ɗakin da ake liyafar, ta ce, “Ran sarki, ya daɗe! Kada ka firgita, kada kuma fuskarka ta turɓune.


Sai Daniyel ya ce wa sarki, “Ran sarki ya daɗe!


Sa'an nan waɗannan shugabanni da muƙaddasai suka ƙulla shawara, suka zo wurin sarki, suka ce masa, “Ran sarki Dariyus ya daɗe!


Zan sa biranenku su zama kangwaye, in mai da wuraren yin sujada kufai, ba zan shaƙi ƙanshin turarenku ba.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan