Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Nehemiya 2:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Ni kuwa ina riƙe da finjalin sarki. Wata rana a watan Nisan, a shekara ta ashirin ta sarautar sarki Artashate, sa'ad da na kai masa ruwan inabi, sai na ɗauki ruwan inabin, na ba shi. Ni ban taɓa ɓata fuskata a gabansa a dā ba, sai wannan karo.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 A watan Nisan a shekara ta ashirin ta mulkin Sarki Artazerzes, sa’ad aka kawo masa ruwan inabi, sai na karɓa na ba shi. Ban taɓa ɓata fuskata a gabansa ba, sai wannan karo.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Nehemiya 2:1
9 Iomraidhean Croise  

Finjalin Fir'auna na hannuna, sai na ɗauki 'ya'yan inabi na matse su cikin finjalin Fir'auna, na sa finjalin a hannun Fir'auna.”


Ya komar da shugaban masu shayarwa a matsayinsa na shayarwa, ya kuwa miƙa finjali a hannun Fir'auna,


A zamanin Artashate kuma sai Bishlam, da Mitredat, da Tabeyel, da magoya bayansu suka rubuta wa Artashate Sarkin Farisa takarda da harufan Suriya, aka fassara ta.


Bayan wannan a zamanin Artashate Sarkin Farisa, sai Ezra ya gane da asalinsa, wato shi na ɗan Seraiya, da Azariya, da Hilkiya,


A shekara ta bakwai kuma ta sarautar sarki Artashate, waɗansu mutanen Isra'ila, da waɗansu firistoci, da Lawiyawa, da mawaƙa, da matsaran ƙofa, da ma'aikatan Haikali, suka taho Urushalima.


Labarin Nehemiya ɗan Hakaliya ke nan. Ya zama fa a watan Kisle a shekara ta ashirin, sa'ad da ni Nehemiya nake a fādar Shushan, wato alkarya,


Ya Ubangiji, ka kasa kunne ga addu'ar bawanka, da addu'o'in bayinka, waɗanda suke jin daɗin girmama sunanka. Ka ba bawanka nasara yau ka sa ya sami tagomashi a gaban mutumin nan.”


A watan fari, wato watan Nisan, a shekara ta goma sha biyu ta sarautar sarki Ahasurus, sai suka yi ta jefa Fur, wato kuri'a, a gaban Haman kowace rana da kowane wata har kuri'a ta faɗo a kan watan goma sha biyu, wato watan Adar.


Sai ka sani, ka kuma gane, daga lokacin da aka umarta a sāke gina Urushalima har zuwa lokacin da shugaba, Masiha, zai zo, za a yi shekara arba'in da tara, da shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu. Za a sāke gina ta a yi mata tituna da kagara.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan