Nehemiya 11:3 - Littafi Mai Tsarki3 Waɗannan su ne shugabannin lardi waɗanda suka zauna a Urushalima, amma a garuruwan Yahuza kowa ya zauna a mahallinsa a garuruwansu, wato Isra'ila, da firistoci, da Lawiyawa, da ma'aikatan Haikali, da zuriyar barorin Sulemanu. Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 20203 Waɗannan su ne shugabannin yankuna waɗanda suka zauna a Urushalima (ko da yake waɗansu Isra’ilawa, da firistoci, da Lawiyawa, da ma’aikatan haikali, da zuriyar bayin Solomon, suka yi zama a cikin garuruwan Yahuda, kowanne a mallakarsa cikin garuruwa dabam-dabam, Faic an caibideil |
Ga lissafin ma'aikatan Haikali da suka komo. Zuriyar Ziha, da zuriyar Hasufa, da zuriyar Tabbawot Zuriyar Keros, da zuriyar Siyaha, da zuriyar Fadon Zuriyar Lebana, da zuriyar Hagaba, da zuriyar Akkub Zuriyar Hagab, da zuriyar Shamlai, da zuriyar Hanan Zuriyar Giddel, da zuriyar Gahar, da zuriyar Rewaiya Zuriyar Rezin, da zuriyar Nekoda, da zuriyar Gazam Zuriyar Ussa, da zuriyar Faseya, da zuriyar Besai Zuriyar Asna, da Me'uniyawa, da Nefushiyawa Zuriyar Bakbuk, da zuriyar Hakufa da zuriyar Harhur Zuriyar Bazlut, da zuriyar Mehida, da zuriyar Harsha Zuriyar Barkos, da zuriyar Sisera, da zuriyar Tema Zuriyar Neziya, da zuriyar Hatifa.
Ma'aikatan Haikali da suka komo daga zaman talala, su ne Zuriyar Ziha, da Hasufa, da Tabbawot, Keros, da Siyaha, da Fadon, Lebana, da Hagaba, da Shamlai, Hanan, da Giddel, da Gahar, Rewaiya, da Rezin, da Nekoda, Gazam, da Uzza, da Faseya, Besai, da Me'uniyawa, da Nefushiyawa, Bakbuk, da Hakufa, da Harkur, Bazlut, da Mehida, da Harsha, Barkos, da Sisera, da Tema, Neziya, da Hatifa.