Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Nehemiya 10:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Waɗanda suka fara sa hannu a takardar alkawarin, su ne mai mulki, wato Nehemiya ɗan Hakaliya, da Zadakiya,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Waɗanda suka buga hatimin su ne, Nehemiya ɗan Hakaliya, wanda yake gwamna. Zedekiya

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Nehemiya 10:1
11 Iomraidhean Croise  

Sarki ya tsaya kusa da ginshiƙi ya yi alkawari ga Ubangiji, cewa zai bi Ubangiji da zuciya ɗaya, da dukan ransa. Zai kiyaye umarnansa, da farillansa, da dokokinsa, ya bi maganar alkawarin da aka rubuta a littafin. Dukan jama'a kuma suka yi alkawarin.


Bari mu yi alkawari da Allahnmu, mu kori dukan waɗannan mata da 'ya'yansu, bisa ga shawarar shugabanni da waɗanda suke rawar jiki saboda umarnin Allah. Bari mu yi alkawari bisa ga doka.


Sai mai mulki ya ce ba za su ci abinci mafi tsarki ba, sai firist ya shawarci Urim da Tummim tukuna, wato kamar kuri'a ke nan.


Labarin Nehemiya ɗan Hakaliya ke nan. Ya zama fa a watan Kisle a shekara ta ashirin, sa'ad da ni Nehemiya nake a fādar Shushan, wato alkarya,


sa'an nan firistoci, wato Seraiya, da Azariya, da Irmiya, Fashur, da Amariya, da Malkiya, Hattush, da Shebaniya, da Malluki, Harim, da Meremot, da Obadiya, Daniyel, da Ginneton, da Baruk, Meshullam, da Abaija, da Miyamin, Mawaziya, da Bilgai, da Shemaiya.


Suka ce, “Ba za mu aurar wa mutanen ƙasar da 'ya'yanmu mata ba. Ba kuma za mu auro wa 'ya'yanmu maza 'ya'yansu mata ba.


Sai mai mulki ya faɗa musu kada su ci abinci mafi tsarki, sai an sami firist wanda zai yi tambaya ta wurin Urim da Tummin tukuna.


Da yawa daga cikin jama'a suka ba da taimako domin biyan aikin gyaran Haikali. Mai mulki ya ba da zinariya darik dubu (1,000) kwanonin wanke hannu guda hamsin rigunan firistoci ɗari biyar da talatin Shugabannin iyali suka ba da zinariya darik dubu ashirin (20,000) azurfa maina dubu biyu da ɗari biyu (2,200) Sauran jama'a suka ba da zinariya darik dubu ashirin (20,000) azurfa maina dubu biyu (2,000) rigunan firistoci guda sittin da bakwai.


Nehemiya kuwa wanda yake mai mulki, da Ezra, firist da magatakarda, da Lawiyawa waɗanda suka fassara wa jama'a dokokin, suka ce wa dukan jama'a, “Wannan rana tsattsarka ce, ta Ubangiji Allahnku, kada ku yi baƙin ciki ko kuka.” Gama mutane duka sai kuka suke sa'ad da aka karanta musu dokokin.


“Saboda wannan duka muke yin alkawari mai ƙarfi a rubuce. Shugabanninmu kuwa, da Lawiyawanmu, da firistocinmu, suka buga hatimi, suka sa hannu.”


Musa kuwa ya rubuta dukan dokokin Ubangiji. Kashegari da sassafe ya gina bagade a gindin dutsen, da kuma ginshiƙai goma sha biyu bisa ga yawan kabilai goma sha biyu na Isra'ila.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan