Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Nehemiya 1:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Amma idan kun juyo wurina, kun kiyaye umarnaina, kun aikata su, ko da yake an warsatsar da ku can nesa, zan tattaro ku, in kawo ku wurin da na zaɓa domin in sa sunana ya kahu a wurin.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 amma in kuka dawo gare ni kuka kuma yi biyayya da umarnaina, to, ko mutanenku da aka kwasa zuwa zaman bauta suna can wuri mafi nisa, zan tattara su daga can in kawo su wurin da na zaɓa yă zama wurin zama don Sunana.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Nehemiya 1:9
28 Iomraidhean Croise  

Idan sun komo gare ka da zuciya ɗaya, da dukan ransu a ƙasar abokan gabansu waɗanda suka kai su bauta, suka yi addu'a gare ka, suna fuskantar ƙasarsu wadda ka ba kakanninsu, da birnin da ka zaɓa, da Haikalin da na gina saboda sunanka,


Ubangiji ya ce masa, “Na ji addu'arka da roƙe-rokenka da ka yi a gare ni, saboda haka na tsarkake Haikalin nan da ka gina, na kuma sa sunana ya kasance a wurin har abada. Idanuna da zuciyata kuma za su kasance a wurin kullum.


Ku ce masa, “Ka cece mu, ya Allah Mai Cetonmu, Ka tattara mu, ka kuɓutar da mu daga al'ummai, Domin mu gode maka, Mu kuma yabi sunanka mai tsarki.”


Allah wanda ya sa sunansa ya kasance a Urushalima, ya hamɓarar da kowane sarki, ko al'umma waɗanda za su sāke wannan doka don su lalatar da Haikalin Allah da yake a Urushalima. Ni Dariyus na kafa wannan doka. Lalle ne a kiyaye dokata sarai.”


Ka cece mu, ya Ubangiji Allahnmu, Ka komo da mu daga cikin sauran al'umma, Domin mu yabi sunanka mai tsarki, Mu kuma yi murna mu yi maka godiya.


Ya komo da ku daga ƙasashen waje, Daga gabas da yamma, kudu da arewa.


Ubangiji yana rayar da Urushalima, Yana komo da waɗanda aka kai su baƙunci a wata ƙasa.


Ubangiji zai ɗaga tuta, alama ce ta nuna wa sauran al'umma, ya sāke tattara jama'ar Isra'ila da ta Yahuza waɗanda aka warwatsa, ya sāke komo da su daga kusurwoyi huɗu na duniya.


A wannan rana Ubangiji kansa zai hukunta jama'arsa, Isra'ila, daga wannan iyakar ƙasa zuwa waccan, tun daga Yufiretis har zuwa iyakar Masar. Zai raba tsakanin nagari da mugu.


Haka Ubangiji Allah, shi wanda ya tattara Isra'ilawa korarru, ya faɗa, ya ce, “Zan ƙara tattaro waɗansu, bayan waɗanda na riga na tattara.”


Bayan na tumɓuke su kuma, zan sāke yi musu jinƙai, in komar da su, kowanne zuwa gādonsa.


“Ku komo, ya ku mutane marasa aminci, Gama ni ne Ubangijinku. Zan ɗauki mutum guda daga kowane gari, In ɗauki mutum biyu daga kowane iyali, Zan komo da su zuwa Dutsen Sihiyona.


“Ku ji maganar Ubangiji, Ya ku al'ummai, Ku yi shelarsa har a ƙasashen da suke nesa, na gāɓar teku. Ku ce, ‘Shi wanda ya warwatsa Isra'ila zai tattaro ta, Zai kiyaye ta kamar yadda makiyayi yakan kiyaye garkensa.’


Ga shi, zan tattaro su daga dukan ƙasashe inda na kora su, da fushina, da hasalata, da haushina. Zan komo da su a wannan wuri, zan sa su su zauna lafiya.


Haka Ubangiji ya ce, “Ga shi, jama'a tana fitowa daga ƙasar arewa. Babbar al'umma ce, Ta yunƙuro tun daga manisantan wurare na duniya.


“Domin haka ka ce wa mutanen Isra'ila, ‘Ubangiji ya ce ku tuba, ku rabu da gumakanku, da abubuwanku na banƙyama.


Zan kwaso ku daga cikin al'ummai, in tattaro ku daga dukan ƙasashe, in kawo ku cikin ƙasarku.


“Idan kun bi dokokina, kun kiyaye umarnaina, kun aikata su,


Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, zan ceci mutanena daga ƙasar gabas da ƙasar yamma.


Zai kuwa aiko mala'ikunsa su busa ƙaho mai tsananin ƙara, su kuma tattaro zaɓaɓɓunsa daga gabas da yamma, kudu da arewa, wato, daga wannan bangon duniya zuwa wancan.”


Idan wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa don ya sa sunansa ya yi muku nisa ƙwarai, to, sai ku yanka daga cikin garken shanunku, ko daga tumaki da awaki, waɗanda Ubangiji ya ba ku, kamar yadda na umarce ku. Za ku iya ci yadda kuke bukata a garuruwanku.


Amma sai ku nemi wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa daga cikin kabilanku duka, inda zai sa sunansa, ya mai da shi wurin zamansa.


“Sa'ad da duk waɗannan abubuwa suka same ku, wato albarka da la'ana waɗanda na sa a gabanku, in kun tuna da su a zuciyarku a duk inda kuke cikin al'ummai inda Ubangiji Allahnku ya kora ku,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan