Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Nehemiya 1:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Da na ji wannan labari, sai na zauna, na yi kuka. Na yi kwanaki ina baƙin ciki, na yi ta azumi da addu'a a gaban Allah na Sama.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Da na ji waɗannan abubuwa, sai na zauna na yi kuka. Na yi kwanaki ina makoki da azumi, na kuma yi addu’a a gaban Allah na sama.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Nehemiya 1:4
22 Iomraidhean Croise  

Dawuda kuwa ya roƙi Allah saboda yaron. Ya yi azumi. Ya shiga ya kwanta a ƙasa dukan dare.


da yake zuciyarka mai tuba ce, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gabana sa'ad da ka ji yadda na yi magana gāba da wannan wuri, da kuma mazaunansa, cewa zai zama kufai da la'ana, kai kuwa ka keta tufafinka, ka yi kuka a gabana, hakika na ji kukanka.


Sulemanu ya riga ya yi dakali na tagulla, tsawonsa kamu biyar, fāɗinsa kamu biyar, tsayinsa kamu uku, ya ajiye shi a tsakiyar filin, ya tsaya a kai. Ya durƙusa a gwiwoyinsa, a idon dukan taron jama'ar Isra'ila, ya ɗaga hannuwansa sama,


Ga shelar, “In ji Sairus Sarkin Farisa, Ubangiji, Allah na samaniya ya ba ni sarautar dukan duniya, ya kuma umarce ni in gina masa Haikali a Urushalima, ta ƙasar Yahuza.


Sa'ad da Ezra yake yin addu'a, yana hurta laifi, yana kuka, yana a durƙushe gaban Haikalin Allah, sai babban taron jama'a, mata, da maza, da yara daga Isra'ila suka taru wurinsa. Mutane suka yi kuka mai zafi.


Sa'ad da na ji wannan, sai na yayyage rigata da alkyabbata, na tsittsiga gashin kaina da na gemuna, na zauna a ruɗe.


A lokacin sadakar yamma ɗin, sai na tashi daga yin azumi, da rigata da alkyabbata yagaggu. Na rusuna a gwiwoyina, na ɗaga hannuwana zuwa ga Ubangiji Allahna.


Ni kuwa sai na amsa musu, na ce, “Allah na Sama zai ba mu nasara, saboda haka mu mutanensa za mu tashe, mu kama gini, amma ba ruwanku, ba hakkinku, ba ku da wani abin tunawa a Urushalima.”


Sa'an nan sarki ya ce mini, “To, me kake so?” Sai na yi addu'a ga Allah na Sama,


Sauran al'umma za su ji tsoron Ubangiji, Dukan sarakunan duniya za su ji tsoron ikonsa.


Ku yi wa Allah sa Sama godiya, Gama ƙaunarsa madawwamiyar ce.


A bakin kogunan Babila Muka zauna muka yi ta kuka, Sa'ad da muka tuna da Sihiyona.


A waɗannan kwanaki, ni Daniyel, ina fama da baƙin ciki har mako uku.


Ya faɗa musu su nemi jinƙai daga wurin Allah na Sama game da wannan matsala, domin kada Daniyel da abokansa su halaka tare da sauran masu hikima a Babila.


Sai na mai da hankalina wajen Ubangiji Allah, ina nemansa ta wurin addu'a, da roƙe-roƙe tare da azumi, ina saye da tufafin makoki, na zauna cikin toka.


Sai Yunusa ya ce, “Ni Ba'ibrane ne, ina bin Ubangiji Allah na Sama, wanda ya yi teku da ƙasa.”


Zan tara waɗanda suka yi makoki domin idi, Waɗanda suke tare da ke, Wato waɗanda nawayar zaman talala Ta zamar musu abin zargi.


Ku taya masu farin ciki farin ciki, masu kuka kuwa ku taya su kuka.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan