Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Nehemiya 1:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Sai suka ce mini, “Waɗanda suka tsira, suka koma daga zaman talala, da suke can lardin, suna cikin wahala ƙwarai, suna kuma shan kunya. Garun Urushalima kuma ya rushe, ƙofofi sun ƙone.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Suka ce mini, “Waɗanda suka tsira daga kwasan zuwa zaman bauta da kuma suka komo cikin yankin suna cikin babban damuwa da wulaƙanci. An rushe katangar Urushalima aka kuma ƙone ƙofofin da wuta.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Nehemiya 1:3
33 Iomraidhean Croise  

sai in raba jama'ar Isra'ila da ƙasar da na ba su, Haikalin kuma da na tsarkake domin sunana, zan kawar da shi daga gabana. Jama'ar Isra'ila kuwa za su zama abin karin magana, da abin ba'a a wurin dukan mutane.


Dukan sojojin Kaldiyawa waɗanda suke tare da shugaban, suka rushe garun da yake kewaye da Urushalima.


Suka ƙone Haikalin Allah suke rushe garun Urushalima, suka ƙone dukan fādodinta, suka lalatar da dukan kayanta masu daraja.


Waɗannan su ne mutanen da suka bar lardin Babila suka komo Urushalima da Yahuza daga bautar talala da Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya kai su Babila. Kowa ya koma garinsu.


Muna sanar da sarki, cewa mun tafi lardin Yahuza a wurin Haikalin Allah Mai Girma. Ana ginin Haikalin da manyan duwatsu, ana kuma sa katakai a bango. Aikin yana ci gaba sosai a hannunsu.


Waɗannan su ne shugabannin lardi waɗanda suka zauna a Urushalima, amma a garuruwan Yahuza kowa ya zauna a mahallinsa a garuruwansu, wato Isra'ila, da firistoci, da Lawiyawa, da ma'aikatan Haikali, da zuriyar barorin Sulemanu.


Da na fita, sai na bi ta Ƙofar Kwari zuwa Rijiyar Dila da Ƙofar Juji, na dudduba garun Urushalima, wanda aka rushe, da ƙofofinsa da wuta ta cinye.


Sa'an nan na ce musu, “Kun ga irin wahalar da muke ciki, yadda Urushalima ta zama kango, an kuma ƙone ƙofofinta. Ku zo, mu sāke gina garun Urushalima don mu fita kunya.”


na ce wa sarki, “Ranka ya daɗe, me zai hana fuskata ta ɓaci, da yake birni inda makabartar kakannina take ya zama kango, an kuma ƙone ƙofofinsa da wuta?”


Waɗannan su ne mutanen lardin Yahuza, waɗanda suka komo daga zaman talala da Nebukadnezzar Sarkin Babila ya kai mutane. Sun komo Urushalima da Yahuza. Kowa ya tafi garinsu.


Ahasurus ya yi sarauta daga Hindu har zuwa Habasha, ya mallaki larduna ɗari da ashirin da bakwai.


Sauran al'ummar da take kewaye da mu, Suka maishe mu abin ba'a, suka yi mana dariya, Suka yi mana ba'a.


Idan ba ka iya danne fushinka ba, ka zama mai kasala kamar birnin da ba shi da garuka, yana buɗe don a faɗa masa.


Zan musunci masu mulkin tsattsarkan masujadai, Saboda haka zan jawo wa Isra'ila hallaka, Zan bari a la'anta mutanena su sha zagi!”


“Ga abin da zan yi wa gonar inabina. Zan cire shingen da yake kewaye da ita, in rushe bangon da ya kāre ta, in bar namomin jeji su cinye ta, su tattake ta.


Zan maishe su abin ƙyama da masifa ga mulkokin duniya duka. Za su zama abin zargi, da karin magana, da ba'a, da la'ana a dukan wuraren da zan warwatsa su.


Zan fafare su da takobi, da yunwa, da masifa. Zan maishe su abin ƙyama ga dukan mulkokin duniya. Za su zama abin la'ana, da abin razana, da abin raini, da abin zargi, ga dukan al'ummai, inda na kora su.


Sai Kaldiyawa suka ƙone gidan sarki, da gidajen jama'a. Suka kuma rushe garun Urushalima.


“Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, ‘Kamar yadda na kwararo fushina da hasalata a kan mazaunan Urushalima, haka kuma zan kwararo fushina a kanku sa'ad da kuka tafi Masar. Za ku zama najasa, da abin ƙyama, da la'ana, da abin ba'a. Wannan wuri kuwa ba za ku ƙara ganinsa ba.’


Ku haura, ku lalatar da gonar kurangar inabinta, Amma kada ku yi mata ƙarƙaf, Ku sassare rassanta, Gama su ba na Ubangiji ba ne.


Sojojin Kaldiyawa da suke tare da shugaban matsara, suka rushe dukan garun Urushalima.


A kwanakin wahalarta na rashin wurin zama, Urushalima ta tuna da dukan abubuwanta masu daraja a dā. A lokacin da mutanenta suka fāɗa a hannun maƙiyi, Ba wanda ya taimake ta, Maƙiyanta sun gan ta, Sun yi mata ba'a saboda fāɗuwarta.


Ƙofofinta sun nutse ƙasa, Ya lalatar, ya kakkarya ƙyamarenta, An kai sarkinta da mahukuntanta cikin al'ummai, Inda ba a bin dokokin annabawanta, Ba su kuma samun wahayi daga wurin Ubangiji.


“Ya Ubangiji, ka ji zargi Da dukan dabarun da suke yi mini.


Ya Ubangiji, ka tuna da abin da ya same mu. Ka duba, ka ga yadda muka zama abin kunya!


Zan sa biranenku su zama kangwaye, in mai da wuraren yin sujada kufai, ba zan shaƙi ƙanshin turarenku ba.


Zan sa a kawo muku yaƙi a warwatsa ku a baƙin ƙasashe, ƙasarku za ta zama kufai, biranenku kuwa za su lalace.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan