Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Nehemiya 1:2 - Littafi Mai Tsarki

2 sai Hanani, ɗaya daga cikin 'yan'uwana, ya zo tare da waɗansu mutanen Yahuza. Na kuwa tambaye shi labarin Yahudawan da suka tsira, suka koma daga zaman talala, da labarin Urushalima.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Hanani, ɗaya daga cikin ’yan’uwana, ya zo daga Yahuda tare da waɗansu mutane. Na kuwa tambaye shi game da raguwar Yahudawan da suka tsira daga kwasan zuwa zaman bauta, da kuma game da Urushalima.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Nehemiya 1:2
12 Iomraidhean Croise  

Akwai ramummukan kalo da yawa a kwarin Siddim. Da Sarkin Saduma da na Gwamrata suka sheƙa da gudu sai waɗansunsu suka fāɗa cikin ramummukan, sauran kuwa suka gudu zuwa dutsen.


Nebukadnezzar ya kwashe dukan mutanen Urushalima, da dukan hakimai da dukan jarumawa, da masu sana'a, da maƙera, har sun kai dubu goma (10,000). Ba wanda ya ragu sai dai matalautan ƙasar.


Amma shugaban sojojin ya bar matalautan ƙasar su zama masu gyaran inabi, da masu noma.


Za mu sake ƙetare umarninka, mu yi aurayya da mutanen da suke yin waɗannan ƙazanta? Ba za ka yi fushi da mu, ka ƙone mu da fushinka har babu ringi ba?


sai na ba ɗan'uwana, Hanani, da Hananiya, shugaban kagara, aikin riƙon Urushalima. Shi Hananiya mai aminci ne, mai tsoron Allah, fiye da sauran mutane.


Ba waɗansu daga cikin mutanen Yahuza da suka ragu, waɗanda suka zo Masar da zama, da za su tsere ko su rayu. Ba wani daga cikinsu da zai koma Yahuza inda suke marmarin komawa da zama, ba wanda zai koma, sai dai 'yan gudun hijira.”


Waɗansunku da suka tsere za su tuna da ni cikin al'ummai inda aka kai su bautar talala yadda raina ya ɓaci saboda zuciyarsu ta rashin imani wadda ta rabu da ni, da idanunsu masu zina da suke bin gumaka. Za su kuwa ji ƙyamar kansu saboda mugayen abubuwa da suka aikata.


Idan akwai waɗanda suka tsere, za a same su a kan duwatsu kamar kurciyoyin kwaruruka, suna baƙin ciki dukansu, kowa yana baƙin ciki saboda laifinsa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan