Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 9:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Yau za ku sani Ubangiji Allahnku yake muku ja gaba sa'ad da kuke hayewa. Shi wuta ne mai cinyewa, zai hallaka su, ya rinjayar muku su, domin ku kore su, ku hallaka su nan da nan kamar yadda Ubangiji ya alkawarta muku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Amma ku zauna da sani a yau, cewa Ubangiji Allahnku, shi ne wanda ya ƙetare ya sha gabanku kamar wuta mai cinyewa. Zai hallaka su, zai rinjaye su a gabanku. Za ku kore su, ku kuma hallaka su nan da nan, yadda Ubangiji ya yi muku alkawari.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 9:3
34 Iomraidhean Croise  

Mala'ikana zai wuce gabanku, ya bi da ku inda Amoriyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Kan'aniyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa suke, zan kuma hallakar da su ƙaƙaf.


Isra'ilawa suka ga ɗaukakar Ubangiji kamar wuta mai cinyewa a bisa ƙwanƙolin dutsen.


Ba zan ƙara yin fushi da gonar inabin ba. Da ma a ce akwai ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya in yi faɗa da su, da na ƙone su ƙurmus.


Ana iya ganin ikon Allah da ɗaukakarsa daga nesa! Wuta da hayaƙi suna nuna fushinsa. Ya yi magana, maganarsa tana ƙuna kamar wuta.


Ubangiji zai bar kowane mutum ya ji maɗaukakiyar muryarsa, ya kuma ji ƙarfin fushinsa. Za a ga harsunan wuta, gizagizai za su ɓarke, za a yi ƙanƙara, da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya.


An riga an shirya wurin ƙonawa don Sarkin Assuriya. An tsiba itace cike da wurin. Kamar kibritu, numfashin Ubangiji zai cinna masa wuta.


Jama'ar Sihiyona cike da zunubi suke, suna ta rawar jiki don tsoro. Suka ce, “Hukuncin Allah kamar wuta ce mai ci har abada. Akwai wani daga cikinmu da zai iya tsira daga irin wannan wuta?”


“Wanda zai huda garu, shi zai yi musu jagora, Za su fita ƙofar, su wuce, su fice ta cikinta. Sarkinsu zai wuce gabansu, Ubangiji kuma yana kan gaba.”


Ya kira taro ya ce musu, “Ku saurara, ku fahimta.


Sai ya sāke kiran jama'a, yă ce musu, “Ku saurare ni dukanku, ku kuma fahimta.


To, me kuma za mu ce a game da haka? Da yake Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu?


Don haka kada ku zama marasa azanci, sai dai ku fahimci abin da yake nufin Ubangiji.


Ubangiji Allahnku wanda yake tafiya tare da ku, shi kansa zai yi yaƙi dominku kamar yadda ya yi muku a Masar a kan idonku.


“Sa'ad da kuka tafi yaƙi da magabtanku, idan kun ga dawakai, da karusai, da sojoji da yawa fiye da naku, kada ku ji tsoronsu. Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar yana tare da ku.


Ubangiji Allahnku yana tafe tare da ku, zai yaƙi magabtanku dominku, ya ba ku nasara.’


Gama Ubangiji Allahnku wuta ne mai cinyewa, shi kuma mai kishi ne.


Sai ku hallaka dukan mutanen da Ubangiji Allahnku ya bashe su a hannunku. Kada ku ji tausayinsu. Kada kuma ku bauta wa gumakansu, don kada su zamar muku tarko.


Ubangiji Allahnku zai kori waɗannan al'ummai a gabanku da kaɗan da kaɗan. Ba za ku hallaka su gaba ɗaya ba, don kada namomin jeji su yaɗu, su dame ku.


Sai ku sani fa, ba saboda adalcinku ne Ubangiji Allahnku yake ba ku kyakkyawar ƙasan nan don ku mallake ta ba, gama ku jama'a ce mai taurinkai.”


yana ta sāka wa waɗanda suke ƙi sanin Allah, da kuma waɗanda suka ƙi bin bisharar Ubangijinmu Yesu.


domin Allahnmu wuta ne mai cinyewa.


Joshuwa kuma ya ci dukan biranen sarakunan nan, da dukan sarakunansu. Ya kashe su da takobi, ya hallakar da su ƙaƙaf kamar yadda Musa bawan Ubangiji ya umarta.


Ubangiji kuwa ya ba da su a hannun Isra'ilawa, suka kuwa ɗibge su, suka runtume su, har zuwa Sidon Babba, da Misrefot-mayim, har zuwa gabashin kwarin Mizfa. Suka karkashe su ƙaƙaf.


Saboda haka sai ka ba ni ƙasar tuddai da Ubangiji ya ambata a ranan nan, gama a wannan rana ka ji yadda gwarzaye suke a can da manyan birane masu garu, mai yiwuwa ne Ubangiji zai kasance tare da ni, in kore su kamar yadda Ubangiji ya faɗa.”


Ga shi, akwatin alkawari na Ubangijin dukkan duniya yana wucewa a gabanku zuwa cikin Urdun.


(Da kaka Urdun yakan yi cikowa makil.) Jama'a fa, suka tashi daga alfarwansu don su haye Urdun. Firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari suna gaba. Da firistocin suka tsoma ƙafafunsu cikin ruwa daga gefe,


Debora ta ce wa Barak, “Tashi! Gama wannan ita ce ranar da Ubangiji ya ba da Sisera a hannunka, gama Ubangiji yana bi da kai!” Sai Barak ya gangaro daga Dutsen Tabor da mutum dubu goma (10,000) biye da shi.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan