Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 9:1 - Littafi Mai Tsarki

1 “Ku ji, ya Isra'ilawa, yau kuna kan haye Kogin Urdun, don ku kori al'ummai waɗanda suka fi ku yawa, sun kuwa fi ku ƙarfi. Suna da manyan birane masu dogon garu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Ku ji, ya Isra’ila. Kuna gab da haye Urdun, ku shiga, ku kuma kori al’ummai da suka fi ku yawa, suka kuma fi ku ƙarfi, masu manyan biranen da suke da katangar da suka yi tsaye zuwa sama.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 9:1
24 Iomraidhean Croise  

Sai suka ce, “Ku zo, mu gina wa kanmu birni, da hasumiya wadda ƙwanƙolinta zai kai can cikin sammai domin mu yi wa kanmu suna, domin kada mu warwatsu ko'ina bisa duniya.”


Da mutane suka ga Musa ya yi jinkirin saukowa daga dutsen, sai suka taru wurin Haruna, suka ce masa, “Tashi, ka yi mana allahn da zai shugabance mu, gama ba mu san abin da ya faru da Musa ɗin wanda ya fisshe mu daga ƙasar Masar ba.”


“ ‘Itacen ya yi girma, ya ƙasaita, Ƙwanƙolinsa ya kai har sama, Ana iya ganinsa ko'ina a duniya.


“Amma ga shi, saboda ku na hallakar da Amoriyawa, Dogayen mutanen nan masu kama da itatuwan al'ul, Ƙarfafa kuma kamar itatuwan oak, Na hallaka su ƙaƙaf.


Suka haura ta wajen Negeb, suka isa Hebron inda Ahimaniyawa, da Sheshaiyawa, da Talmaiyawa, zuriyar ƙarfafan mutanen da ake kira Anakawa suke zaune. (An gina Hebron da shekara bakwai kafin a gina Zowan a Masar.)


ya faɗa wa jama'ar Isra'ila, “Sa'ad da kuka haye Urdun zuwa ƙasar Kan'ana,


Ta ƙaƙa za mu hau? Gama 'yan'uwanmu sun narkar da zuciyarmu da cewa, mutanen sun fi mu girma, sun kuma fi mu ƙarfi. Biranensu kuma manya manya ne, da gine-gine masu tsayi ƙwarai. Har ma sun ga Anakawa a wurin.’


sa'an nan Ubangiji zai kori al'umman nan duka a gabanku. Za ku kori al'umman da suka fi ku yawa da ƙarfi.


Gama za ku haye Urdun, ku shiga ƙasar da za ku mallaka, wadda Ubangiji Allahnku yake ba ku. Sa'ad da kuka mallake ta, kuka zauna a ciki,


Bayan da kuka haye Urdun, kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, sai ku kakkafa manyan duwatsu, ku yi musu shafe da farar ƙasa.


“A wancan lokaci ne na yi muku umarni, na ce, ‘Ubangiji Allahnku ya ba ku wannan ƙasa, ku mallake ta. Dukan mayaƙanku za su haye da shirin yaƙi a gaban 'yan'uwanku, Isra'ilawa.


“Yanzu, ya Isra'ilawa, sai ku kiyaye dokoki da farillai da nake koya muku don ku rayu, ku shiga ku kuma mallaki ƙasar da Ubangiji Allah na kakanninku suke ba ku.


Ya kori al'ummai a gabanku waɗanda suka fi ku girma da iko, ya kawo ku a ƙasarsu, ya ba ku ita abar gādo kamar yadda yake a yau.


“Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya kai ku ƙasar da ya rantse wa kakanninku Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, zai ba ku manyan birane masu kyau waɗanda ba ku ne kuka gina ba,


“Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya kai ku ƙasar da kuke shiga ku mallake ta, zai korar muku da al'ummai da yawa, su Hittiyawa, da Girgashiyawa, da Amoriyawa, da Kan'aniyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, al'umma bakwai ke nan, waɗanda suka fi ku yawa, da kuma ƙarfi.


“Ku shiga zango, ku umarci jama'a, ku ce, ‘Ku shirya wa kanku guzuri, gama nan gaba da kwana uku za ku haye Kogin Urdun don ku mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku.’ ”


har lokacin da Ubangiji ya hutar da 'yan'uwanku kamarku, su kuma su mallaki ƙasa wadda Ubangiji Allahnku yake ba su, a sa'an nan za ku koma zuwa ƙasar da take mulkinku, ku mallake ta, wato ƙasar da Musa, bawan Ubangiji, ya ba ku a hayin Urdun wajen gabas.”


Saboda haka sai ka ba ni ƙasar tuddai da Ubangiji ya ambata a ranan nan, gama a wannan rana ka ji yadda gwarzaye suke a can da manyan birane masu garu, mai yiwuwa ne Ubangiji zai kasance tare da ni, in kore su kamar yadda Ubangiji ya faɗa.”


(Da kaka Urdun yakan yi cikowa makil.) Jama'a fa, suka tashi daga alfarwansu don su haye Urdun. Firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari suna gaba. Da firistocin suka tsoma ƙafafunsu cikin ruwa daga gefe,


sai ruwan da yake gangarowa ya tsaya, ya tattaru wuri ɗaya, ya yi soro daga nesa kusa da Adam, birnin da yake kusa da Zaretan. Ruwan kuma da yake gangarowa zuwa Tekun Araba, wato Tekun Gishiri, aka yanke shi ɗungum. Jama'a kuwa suka haye daura da Yariko.


Ya kuma ce wa firistocin, “Ku ɗauki akwatin alkawari ku wuce gaban jama'ar.” Sai suka ɗauki akwatin alkawari suka wuce gaban jama'a.


Rana ta goma ga watan ɗaya jama'a suka haye Urdun, suka yi zango a Gilgal a gabashin iyakar Yariko.


Ya ce musu, “Wuce gaban akwatin Ubangiji Allahnku zuwa tsakiyar Urdun, ko wannenku ya ɗauki dutse a kafaɗarsa, don kowace kabila ta Isra'ila.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan