Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 8:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Ƙasa mai alkama, da sha'ir, da inabi, da ɓaure, da rumman. Ƙasa ce mai itatuwan zaitun da zuma.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 ƙasa mai alkama da sha’ir, inabi da ɓaure, rumman, man zaitun da zuma;

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 8:8
23 Iomraidhean Croise  

Zai ɗaure aholakinsa a kurangar inabi, A kuranga mafi kyau, Zai wanke tufafinsa da ruwan inabi, Ruwan inabi ja wur kamar jini.


Rekab da Ba'ana kuwa, suka laɓaɓa, suka shiga kamar suna neman alkama.


Sulemanu kuwa yakan ba Hiram alkama mudu dubu ashirin (20,000), da tattaccen man zaitun ma'auni dubu ashirin (20,000) kowace shekara domin ya ciyar da mutanensa.


har lokacin da zan zo in kwashe ku, in kai ku wata ƙasa mai kama da taku, ƙasa mai yalwar hatsi, da ruwan inabi, da abinci, da gonakin inabi, da itatuwan zaitun, da zuma, don ku rayu, kada ku mutu! Kada kuma ku yarda Hezekiya ya yaudare ku da cewa Ubangiji zai cece ku.


Yakan kiyaye kan iyakar ƙasarki lafiya, Yakan kuma ƙosar da ke da alkama mafi kyau.


Zan ciyar da ku da kyakkyawar alkama, In ƙosar da ku da zuma.”


“A lokacin nan, waɗannan kyawawan gonakin inabi waɗanda suke da kurangar inabi dubu, kuɗin kowace gonar inabi azurfa dubu guda ne, gonakin za su cika da ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya.


Na kawo su zuwa ƙasa mai dausayi, Don su more ta su ci amfaninta, Amma da suka shiga, sun ƙazantar mini da ita, Suka sa ƙasar da na gādar musu ta zama abar ƙyama.


Za su cinye amfanin gonakinku da abincinku. Za su ƙare 'ya'yanku mata da maza. Za su cinye garkunanku na tumaki, da na awaki, da na shanu, Za su kuma cinye 'ya'yan inabinku da na ɓaurenku. Za su hallaka biranenku masu kagara da takobi, waɗanda kuke fariya da su.


Mutanen Yahuza da na ƙasar Isra'ila abokan cinikinki ne. Sun sayi kayan cinikinki da alkama, da zaitun, da 'ya'yan ɓaure, da zuma, da mai, da ganyaye masu ƙanshi.


Ƙasa kuma za ta amsa wa hatsi, da ruwan inabi, da mai, Su ma za su amsa wa Yezreyel.


“Amma ba ta sani ni nake ba ta hatsi, da ruwan inabi, da mai, Da azurfa, da zinariya da yawa Waɗanda suka bauta wa gunkin nan Ba'al da su ba.


Kowa zai zauna gindin kurangar inabinsa da gindin ɓaurensa. Ba wanda zai tsoratar da shi, Gama Ubangiji Mai Runduna ne ya faɗa.


Ko da yake itacen ɓaure bai yi toho ba, Ba kuma 'ya'ya a kurangar inabi, Zaitun kuma bai ba da amfani ba, Gonaki ba su ba da abinci ba, An kuma raba garken tumaki daga cikin garke, Ba kuma shanu a turaku,


Da suka isa Kwarin Eshkol, sai suka datse reshe guda na nonon inabi da 'ya'ya cunkus. Suka rataya a sanda, mutum biyu suka ɗauka a kafaɗunsu. Suka kuma kawo rumman da ɓaure.


Sai suka tattara gutsattsarin gurasar nan biyar na sha'ir da suka saura bayan kowa ya ci, suka cika kwando goma sha biyu.


“Ga wani ɗan yaro nan da gurasa biyar na sha'ir, da kuma kifi biyu. Amma me waɗannan za su yi wa mutane masu yawa haka?”


“Ya sa shi ya hau kan tuddai, Ya ci amfanin ƙasa, Ya sa shi ya sha zuma daga dutse, Ya ba shi mai daga dutsen ƙanƙara.


Ya sami kindirmo daga shanu, Da madara daga garken tumaki da na awaki, Da kitse daga 'yan raguna, da raguna, Da bijimai, da bunsurai daga Bashan, Da alkama mafi kyau. Ka sha ruwan inabi jaja wur, mai kyau.


Don haka, ku ji, ya Isra'ilawa, ku lura, ku kiyaye su domin zaman lafiyarku, domin kuma ku riɓaɓɓanya ƙwarai a ƙasar da take mai yalwar abinci yadda Ubangiji Allah na kakanninku ya alkawarta muku.


Ubangiji Allahnku zai kai ku ƙasa mai kyau. Ƙasa mai rafuffukan ruwa da maɓuɓɓugai, da idanun ruwa masu ɓuɓɓugowa daga cikin kwari da tudu.


Ƙasa ce inda za ku ci abinci a yalwace, ba za ku rasa kome ba. Ƙasa ce wadda tama ce duwatsunta, ana kuma haƙar tagulla a tuddanta.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan