Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 8:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Ubangiji Allahnku zai kai ku ƙasa mai kyau. Ƙasa mai rafuffukan ruwa da maɓuɓɓugai, da idanun ruwa masu ɓuɓɓugowa daga cikin kwari da tudu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Gama Ubangiji Allahnku yana fitar da ku zuwa cikin ƙasa mai kyau, ƙasa mai rafuffuka da tafkunan ruwa, tare da maɓulɓulai masu gudu a kwari da tuddai;

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 8:7
17 Iomraidhean Croise  

don haka na sauko in cece su daga hannun Masarawa, in fito da su daga cikin wannan ƙasa zuwa kyakkyawar ƙasa mai ba da yalwar abinci, wato ƙasar Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa.


a ran nan na rantse musu, cewa zan fito da su daga ƙasar Masar, zuwa wata ƙasa wadda na samo musu, ƙasar da take da yalwar albarka, wato ƙasa mai albarka duka.


Zai ɗaure aholakinsa a kurangar inabi, A kuranga mafi kyau, Zai wanke tufafinsa da ruwan inabi, Ruwan inabi ja wur kamar jini.


Saboda wannan sai ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin hanyoyinsa, ku ji tsoronsa.


Ƙasa mai alkama, da sha'ir, da inabi, da ɓaure, da rumman. Ƙasa ce mai itatuwan zaitun da zuma.


har lokacin da zan zo in kwashe ku, in kai ku wata ƙasa mai kama da taku, ƙasa mai yalwar hatsi, da ruwan inabi, da abinci, da gonakin inabi, da itatuwan zaitun, da zuma, don ku rayu, kada ku mutu! Kada kuma ku yarda Hezekiya ya yaudare ku da cewa Ubangiji zai cece ku.


Sai suka ƙi ƙasan nan mai ni'ima, Saboda ba su gaskata alkawarin Allah ba.


Na kawo su zuwa ƙasa mai dausayi, Don su more ta su ci amfaninta, Amma da suka shiga, sun ƙazantar mini da ita, Suka sa ƙasar da na gādar musu ta zama abar ƙyama.


Sai kuma ta ɗauki irin na ƙasar, ta dasa shi a wuri mai dausayi kusa da ruwa mai yawa. Ta dasa shi kamar itacen wardi.


Idan kuka je za ku tarar da mutane suna zama a sake. Ƙasar kuwa babba ce, tana da dukan abin da ɗan adam yake bukata.”


Ka sa maɓuɓɓugai suka gudano cikin kwaruruka, Ka sa ruwa yana gudu tsakanin tuddai.


Ku saurara in raira muku wannan waƙa, Waƙar abokina da gonar inabinsa. Abokina yana da gonar inabi A wani tudu mai dausayi.


har babban sarki ya sāke zaunar da ku a wata ƙasa mai kama da taku, inda akwai gonakin inabi da za su ba da ruwan inabi, da hatsi don yin gurasa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan