Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 7:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Ga yadda za ku yi da su, za ku rurrushe bagadansu, ku ragargaza al'amudansu, ku sassare ginshiƙansu na tsafi, ku ƙaƙƙone sassaƙaƙƙun siffofinsu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Ga abin da za ku yi da su, za ku rurrushe bagadansu, ku ragargaza keɓaɓɓun duwatsunsu, ku farfashe ginshiƙan Asheransu, ku kuma ƙona gumakansu da wuta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 7:5
16 Iomraidhean Croise  

Suka fitar da gumakan da suke cikin haikalin Ba'al, suka ƙone su.


Filistiyawa suka gudu suka bar gumakansu a wurin. Dawuda kuwa ya yi umarni, aka ƙone su duka.


Ya kawar da baƙin bagadai da masujadai, ya rurrushe ginshiƙai, ya kuma tumɓuke Ashtarot.


Ba za ku rusuna wa allolinsu ba, balle fa ku bauta musu, kada ku yi yadda suke yi. Sai ku hallaka allolinsu ɗungum, ku farfashe keɓaɓɓun duwatsunsu.


Ya ɗauki siffar ɗan maraƙin da suka yi, ya ƙone ta, ya niƙe, ta zama gari, ya barbaɗa a ruwa, ya sa Isra'ilawa su sha.


Sai ku rurrushe bagadansu, ku farfashe al'amudansu, ku sassare gumakansu.


Ba za su ƙara dogara ga bagaden da suka yi da hannuwansu ba, ko kuwa su dogara ga ayyukan hannuwansu, ko keɓaɓɓun wuraren da suke wa gumaka sujada, ko bagadai don ƙona turare.


Ubangiji ya ce, “Kada ku yi wa kanku gumaka, ko ku kafa sassaƙaƙƙiyar siffa, ko al'amudi. Kada kuma ku kafa wata siffa ta dutse a ƙasarku da za ku durƙusa mata, gama ni ne Ubangiji Allahnku.


sai ku kori dukan mazaunan ƙasar daga gabanku ku rurrushe sassaƙaƙƙun duwatsunsu, da siffofinsu na zubi, da masujadansu.


“Kada ku dasa kowane irin itace na tsafi kusa da bagaden Ubangiji Allahnku, wanda za ku gina.


Kada kuma ku kafa al'amudi, abin da Ubangiji Allahnku yake ƙi.”


Sai ku ƙone siffofin gumakansu. Kada ku yi ƙyashin azurfa ko zinariya da aka dalaye su da ita. Kada ku kwashe su, don kada su zamar muku tarko, gama Ubangiji Allahnku yana ƙyamarsu.


Sa'an nan na ɗauki abin zunubin nan, wato siffar maraƙin da kuka yi, na ƙone, na farfashe, na niƙe shi lilis, ya zama kamar ƙura mai laushi, na zubar da garin a rafi wanda yake gangarowa daga dutsen.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan