Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 7:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Gama za su sa 'ya'yanku su bar bina, su bauta wa gumaka. Wannan zai sa Ubangiji ya husata, ya hallaka ku da sauri.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Gama za su juye ’ya’yanku maza daga bina, su bauta waɗansu alloli, fushin Ubangiji kuma zai ƙuna a kanku da sauri, zai kuma hallaka ku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 7:4
14 Iomraidhean Croise  

Da yake abu ne mai sauƙi a gare shi ya bi hanyar zunuban Yerobowam ɗan Nebat, sai ya auro Yezebel 'yar Etba'al, Sarkin Sidon, ya kuma bauta wa gunkin nan Ba'al, ya yi masa sujada.


Kada ka rusuna musu, kada kuwa ka bauta musu, gama ni Ubangiji Allahnka, mai kishi ne. Nakan hukunta 'ya'ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina.


Kada kuma ku auro wa 'ya'yanku maza 'yan matansu 'ya'ya matansu kuma su yi shagulgulan bidi'ar allolinsu, har su sa 'ya'yanku su bi allolinsu.


don kada su koya muku yin abubuwa masu banƙyama waɗanda suka yi wa gumakansu, har ku yi wa Ubangiji Allahnku zunubi.


to, yau na kira sama da duniya su shaida a kanku, cewa lalle za ku hallaka nan da nan cikin ƙasar da za ku haye Urdun zuwa cikinta don ku mallake ta. Ba za ku daɗe cikinta ba, amma za a shafe ku ƙaƙaf.


gama Ubangiji Allahnku wanda yake zaune a tsakiyarku, mai kishi ne, don kada Ubangiji Allahnku ya husata, ya shafe ku daga duniya.


Da suka zo wurin Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa a ƙasar Gileyad, ya ce musu,


Gama idan kun kauce, kun koma da baya, kun haɗa kai da sauran al'umman nan da take tare da ku, har kuka yi aurayya da juna,


Jama'ar Isra'ila kuwa suka yi wa Ubangiji zunubi, wato suka bauta wa gunkin nan mai suna Ba'al.


Ubangiji kuwa ya husata da Isra'ilawa ya ce, “Saboda al'umman nan ta ta da alkawarina wanda na yi da kakanninsu, ba su yi biyayya da maganata ba,


Suka yi aurayya da su, suka kuma yi sujada ga gumakansu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan