Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 7:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya bashe su a hannunku, kuka kuma ci nasara a kansu, sai ku hallaka su sarai. Kada ku yi alkawari da su, kada kuma ku yi musu jinƙai.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Sa’ad da kuma Ubangiji Allahnku ya ba da su gare ku, kuka kuma ci su da yaƙi, sai ku hallaka su ƙaƙaf. Kada ku yi yarjejjeniya da su, kada kuma ku nuna musu jinƙai.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 7:2
45 Iomraidhean Croise  

Ga Allah Maɗaukaki yabo ya tabbata, shi wanda ya ba ka maƙiyanka a tafin hannunka!” Abram kuwa ya ba shi ushiri na duka.


(Gibeyonawa dai ba mutanen Isra'ila ba ne, su Amoriyawan da suka ragu ne, waɗanda Isra'ilawa suka rantse musu, cewa, ba za su kashe su ba. Amma Saul, saboda kishin da yake yi domin mutanen Isra'ila da Yahuza, ya nema ya kashe su duk.)


Ben-hadad ya ce masa, “Biranen da tsohona ya ƙwace daga wurin tsohonka, zan mayar maka. Kai kuma za ka yi karauku a Dimashƙu kamar yadda tsohonka ya yi a Samariya.” Sai Ahab ya ce, “Zan bar ka, ka tafi a kan wannan sharaɗi.” Ya kuwa yi alkawari da shi, sa'an nan ya bar shi, ya tafi.


Bari mu yi alkawari da Allahnmu, mu kori dukan waɗannan mata da 'ya'yansu, bisa ga shawarar shugabanni da waɗanda suke rawar jiki saboda umarnin Allah. Bari mu yi alkawari bisa ga doka.


Suka ƙi su kashe arna, Yadda Ubangiji ya umarta,


“Wanda ya miƙa hadaya ga wani allah, ba ga Ubangiji ba, sai a hallaka shi ɗungum.


Sai Isra'ilawa suka yi wa'adi ga Ubangiji, suka ce, “In hakika, za ka ba da mutanen nan a hannunmu, lalle za mu hallaka biranensu ƙaƙaf.”


Yanzu, sai ku kashe dukan yara maza da kowace mace wadda ta san namiji.


sai ku kori dukan mazaunan ƙasar daga gabanku ku rurrushe sassaƙaƙƙun duwatsunsu, da siffofinsu na zubi, da masujadansu.


kada ku yarda, kada ku saurare shi. Kada kuma ku ji tausayinsa, kada ku haƙura da shi ko ku ɓoye shi.


Hannunku ne zai fara jifansa, sa'an nan sauran jama'a su jajjefe shi, har ya mutu.


Kada ku ji tausayinsa. Ta haka za ku hana zub da jinin marar laifi cikin Isra'ila, don ku sami zaman lafiya.


Ubangiji Allahnmu ya bashe shi a hannunmu, muka ci nasara a kansa, da 'ya'yansa, da dukan mutanensa.


Muka ci dukan garuruwansa, muka hallaka kowane gari, da mata, da maza, da yara, ko ɗaya bai ragu ba.


Gama Ubangiji Allahnku yakan yi yawo cikin sansaninku don ya cece ku, ya ba da magabtanku cikin hannunku. Saboda haka dole ku tsabtace sansaninku don kada Ubangiji ya iske wata ƙazanta a cikinku, ya rabu da ku.”


sai ku yanke hannunta, kada ku ji tausayi.


“Haka fa Ubangiji Allahnmu ya ba da Og, Sarkin Bashan, da dukan jama'arsa a hannunmu. Muka karkashe su duka, ba wanda muka bari da rai.


Ubangiji zai bashe su a gare ku. Za ku yi musu kamar yadda dā na umarce ku.


Allah Madawwami, shi ne wurin zamanka, Madawwaman damatsansa suna tallafarka, Yana kore maka maƙiyanka, Ya ce, ‘Ka hallaka su!’


Sai ku hallaka dukan mutanen da Ubangiji Allahnku ya bashe su a hannunku. Kada ku ji tausayinsu. Kada kuma ku bauta wa gumakansu, don kada su zamar muku tarko.


Yau za ku sani Ubangiji Allahnku yake muku ja gaba sa'ad da kuke hayewa. Shi wuta ne mai cinyewa, zai hallaka su, ya rinjayar muku su, domin ku kore su, ku hallaka su nan da nan kamar yadda Ubangiji ya alkawarta muku.


A wannan rana kuwa Joshuwa ya ci Makkeda da yaƙi, ya kashe mutanenta da sarkinta da takobi, har ba wanda ya ragu. Ya yi wa Sarkin Makkeda kamar yadda ya yi wa Sarkin Yariko.


Ubangiji ya bashe ta da sarkinta a hannun Isra'ilawa, suka kuwa buge ta da takobi, da kowane mutum da yake cikinta, ba su rage kowa cikinta ba. Suka yi wa sarkinta kamar yadda suka yi wa Sarkin Yariko.


Ubangiji ya ba da Lakish a hannun Isra'ilawa suka cinye ta da yaƙi cikin kwana biyu. Suka bugi kowane mutum da yake cikinta da takobi kamar yadda suka yi wa Libna.


Haka nan kuwa Joshuwa ya cinye dukan ƙasar tuddai, da Negeb, da filayen kwaruruka, da gangare, da sarakunansu duka, ba wanda ya ragu, amma ya hallaka su duka kamar yadda Ubangiji, Allah na Isra'ila ya umarta.


Joshuwa kuwa ya cinye sarakunan nan duka da ƙasashensu gaba ɗaya, gama Ubangiji Allah na Isra'ila ya yi yaƙi domin Isra'ilawa.


Ubangiji kuwa ya ba da su a hannun Isra'ilawa, suka kuwa ɗibge su, suka runtume su, har zuwa Sidon Babba, da Misrefot-mayim, har zuwa gabashin kwarin Mizfa. Suka karkashe su ƙaƙaf.


Mutanen kuwa suka ce mata, “Ranmu a bakin naki, idan ba ki tone al'amarinmu ba, za mu yi miki alheri da aminci sa'ad da Ubangiji ya ba mu ƙasar.”


Ubangiji kuma ya ba da hutawa ko'ina kamar yadda ya rantse wa kakanninsu. Babu wani daga cikin abokan gābansu da ya iya ta da kai da su, gama Ubangiji ya ba da abokan gābansu duka a hannunsu.


Sa'ad da Isra'ilawa suka gama karkashe mazaunan Ai duka a jeji inda suka fafare su, sai Isra'ilawa suka koma Ai, suka karkashe waɗanda suke cikinta.


Sai suka amsa wa Joshuwa, suka ce, “Domin bayinka sun ji labari Ubangiji Allahnka ya umarci bawansa Musa ya ba ku ƙasar duka, ku hallaka dukan mazaunan ƙasar a gabanku, don haka muka ji tsoronku ƙwarai saboda rayukanmu, shi ya sa muka yi haka.


Amma Isra'ilawa suka ce wa Hiwiyawa, “Watakila kuna zaune a tsakiyarmu ne, to, ƙaƙa za mu yi muku alkawari?”


Sai 'yan leƙen asirin ƙasar suka ga wani mutum yana fitowa daga cikin birnin, suka ce masa, “Muna roƙonka ka nuna mana hanyar shiga birnin, mu kuwa za mu yi maka alheri.”


Yahuza ya tafi, Ubangiji kuwa ya ba da Kan'aniyawa da Ferizziyawa a gare su, suka kashe mutum dubu goma daga cikinsu a Bezek.


Ku kuma ba za ku yi alkawari da mazaunan ƙasar nan ba, amma za ku rurrushe bagadansu.’ Duk da haka ba ku yi biyayya da maganata ba. Me ke nan kuka yi?


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan