Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 7:12 - Littafi Mai Tsarki

12 “Idan za ku saurari waɗannan farillai, ku kiyaye su, sai Ubangiji Allahnku ya cika alkawarin da ya rantse wa kakanninku, ya kuma ƙaunace ku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 In kuka mai da hankali ga waɗannan dokoki, kuka kuma yi hankali ga bin su, to, Ubangiji Allahnku zai kiyaye alkawarinsa na ƙauna gare ku, kamar yadda ya rantse wa kakanninku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 7:12
19 Iomraidhean Croise  

ya yi addu'a ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, ba wani Allah kamarka cikin Sama a bisa, da cikin duniya a ƙasa, wanda yake cika alkawari, ya nuna ƙauna ga bayinsa, waɗanda suke tafiya a gabansa da zuciya ɗaya.


Na ce, “Ya Ubangiji Allah na Sama, Allah mai girma, mai banrazana, mai cika alkawari, mai nuna madawwamiyar ƙauna ga waɗanda suke ƙaunarka, wato masu kiyaye umarnanka,


“Ya Allah, Allahnmu, da girma kake! Kai mai banrazana ne, cike da iko! Da aminci ka cika alkawaranka da ka alkawarta. Daga lokacin da Sarkin Assuriya ya danne mu, Har yanzu ma, wace wahala ce ba mu sha ba! Sarakunanmu, da shugabanninmu, da firistocinmu, Da annabawanmu, da kakanninmu, Da dukan sauran jama'arka sun sha wahala. Ka san irin wahalar da muka sha.


Ga waɗanda suke riƙe da alkawarinsa da gaskiya, Waɗanda suke biyayya da umarnansa da aminci.


Su hukunta wa al'ummai, kamar yadda Allah ya umarta. Wannan shi ne cin nasarar jama'ar Allah! Yabo ya tabbata ga Ubangiji!


Ya ce, “In za ku himmantu ku yi biyayya da ni, ni da nake Ubangiji Allahnku, sai ku aikata abin da yake daidai a gare ni, ku kuma kiyaye umarnaina da dokokina duka, to, ba zan sa muku cuce-cuce irin waɗanda na sa wa Masarawa ba, gama ni ne Ubangiji da nake warkar da ku.”


Sa'an nan zan cika maganar rantsuwa da na rantse wa kakanninku, da na ce zan ba su ƙasa wadda take cike da albarka kamar yadda yake a yau.’ ” Irmiya ya ce, “Amin, amin, ya Ubangiji.”


Na yi addu'a ga Ubangiji Allahna, na tuba. Na ce, “Ya Ubangiji, Allah maigirma, mai banrazana, kai mai cika alkawari ne, kana ƙaunar masu ƙaunarka waɗanda suke kiyaye dokokinka.


Za ka nuna wa Yakubu aminci, Ga Ibrahim kuma madawwamiyar ƙauna, Kamar yadda ka rantse wa kakanninmu Tun a zamanin dā.


Ya cika faɗarsa ga kakanninmu, Ga Ibrahim da zuriyarsa, har abada.”


Duba, na sa ƙasar a gabanku, sai ku shiga ku mallake ta, ƙasa wadda na rantse wa kakanninku, wato Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, cewa zan ba su, su da zuriyarsu a bayansu.’ ”


“Idan kun yi biyayya da umarnansa waɗanda ya umarce ku da su yau, kun ƙaunaci Ubangiji Allahnku, kun bauta masa da zuciya ɗaya da dukan ranku,


Amma nakan nuna ƙauna ga dubbai waɗanda suke ƙaunata, suna kiyaye umarnaina.


Saboda haka, sai ku kiyaye umarnai, da dokoki, da farillai ku aikata su, wato waɗanda nake umartarku da su yau.”


Domin haka sai ku sani Ubangiji Allahnku shi ne Allah, Allah mai aminci, mai cika alkawari, mai nuna ƙauna ga dubban tsararraki waɗanda suke ƙaunarsa, suna kuma kiyaye umarnansa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan