Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 7:1 - Littafi Mai Tsarki

1 “Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya kai ku ƙasar da kuke shiga ku mallake ta, zai korar muku da al'ummai da yawa, su Hittiyawa, da Girgashiyawa, da Amoriyawa, da Kan'aniyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, al'umma bakwai ke nan, waɗanda suka fi ku yawa, da kuma ƙarfi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya kawo ku ƙasar da kuke shiga don ku mallaka, ya kuma kori al’ummai masu yawa a gabanku; wato, Hittiyawa, Girgashiyawa, Amoriyawa, Kan’aniyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa, al’ummai bakwai masu girma da ƙarfi fiye da ku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 7:1
35 Iomraidhean Croise  

Da yake abu ne mai sauƙi a gare shi ya bi hanyar zunuban Yerobowam ɗan Nebat, sai ya auro Yezebel 'yar Etba'al, Sarkin Sidon, ya kuma bauta wa gunkin nan Ba'al, ya yi masa sujada.


da Yebusiyawa, da Amoriyawa, da Girgashiyawa,


Dukan jama'ar da suka ragu a ƙasar, wato Hittiyawa, da Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, waɗanda Isra'ilawa ba su hallaka ba,


Bayan da aka gama waɗannan abubuwa, sai shugabanni suka zo wurina, suka ce, “Mutanen Isra'ila, da firistoci, da Lawiyawa ba su keɓe kansu daga ƙazantar mutanen ƙasar ba, wato su Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Yebusiyawa, da Ammonawa, da Mowabawa, da Masarawa, da Amoriyawa.


A waɗannan kwanaki kuma na ga waɗansu Yahudawa waɗanda suka auro mata daga Ashdod, da Ammon, da Mowab.


Ya kori mazaunan wurin sa'ad da jama'arsa suka dirkako, Ya rarraba ƙasar ga kabilan Isra'ila, A nan ya ba su izini su zauna a wurin, a cikin alfarwansu.


Cikin girman ɗaukakarka, ka kā da maƙiyanka, ka aika da hasalarka, Ka cinye su kamar ciyawa.


Zan aiki zirnako a gabanku, su kore muku Hiwiyawa, da Kan'aniyawa, da Hittiyawa.


Kada ku ƙulla alkawari da su, ko da allolinsu.


Kada su zauna cikin ƙasarku domin kada su sa ku ku yi mini zunubi, ku bauta wa allolinsu, har abin kuwa ya zamar muku tarko.”


Zan kuwa aiki mala'ika a gabanka. Zan kuma kori Kan'aniyawa da Amoriyawa, da Hittiyawa, da Farizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa.


Sa'an nan zan kawo ku cikin ƙasar da na rantse zan bai wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu. Zan ba ku ita ta zama mallakarku. Ni ne Ubangiji.’ ”


“Sa'ad da kuka shiga ƙasar Kan'ana wadda nake ba ku ku mallaka, zan sa kuturta ta yaɗu a gidajenku.” Sa'an nan Ubangiji ya ba su waɗannan ka'idodi.


Amalekawa suna zaune a Negeb, Hittiyawa kuwa, da Yebusiyawa, da Amoriyawa suna zaune a ƙasar tuddai, Kan'aniyawa suna zaune kusa da teku, da kuma kusa da Kogin Urdun.”


Amma 'yan ƙanananku, waɗanda kuka ce za su zama ganima, su ne zan kai su cikin ƙasar, za su san ƙasar da kuka raina.


Ya kuma hallaka al'umma bakwai a ƙasar Kan'ana, sai ya raba musu ƙasar tasu gādo, suka zauna har shekara arbaminya da hamsin.


Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya kai ku cikin ƙasar da za ku shiga ku mallake ta, sai ku ɗibiya albarkar a Dutsen Gerizim, ku ɗibiya la'anar kuma a Dutsen Ebal.


“Sa'ad da kuka tafi yaƙi da magabtanku, idan kun ga dawakai, da karusai, da sojoji da yawa fiye da naku, kada ku ji tsoronsu. Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar yana tare da ku.


“Amma kada ku bar kome da rai a garuruwan mutanen nan da Ubangiji Allahnku yake ba ku su gādo.


Sa'ad da na kawo su a ƙasar da take da yalwar abinci, wadda na rantse zan ba kakanninsu, har suka ci, suka ƙoshi, suka yi ƙiba, za su juya, su bi gumaka, su bauta musu. Za su raina ni, su tā da alkawarina.


Ubangiji Allahnku shi ne zai yi gaba ya haye, ya hallaka al'umman da take gabanku don ku ci su. Joshuwa ne zai shugabance ku, ya haye kamar yadda Ubangiji ya faɗa.


Ya kori al'ummai a gabanku waɗanda suka fi ku girma da iko, ya kawo ku a ƙasarsu, ya ba ku ita abar gādo kamar yadda yake a yau.


“Waɗannan su ne umarnai, da dokoki, da farillai waɗanda Ubangiji Allahnku ya umarce ni in koya muku domin ku kiyaye su a ƙasar da kuke hayewa zuwa ciki don ku mallake ta,


“Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya kai ku ƙasar da ya rantse wa kakanninku Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, zai ba ku manyan birane masu kyau waɗanda ba ku ne kuka gina ba,


Zai kuwa kori maƙiyanku a gabanku kamar yadda ya alkawarta.


Ya fisshe mu daga wurin, ya bi da mu zuwa ƙasar da ya alkawarta wa kakanninmu zai ba mu.


“Ku ji, ya Isra'ilawa, yau kuna kan haye Kogin Urdun, don ku kori al'ummai waɗanda suka fi ku yawa, sun kuwa fi ku ƙarfi. Suna da manyan birane masu dogon garu.


Yau za ku sani Ubangiji Allahnku yake muku ja gaba sa'ad da kuke hayewa. Shi wuta ne mai cinyewa, zai hallaka su, ya rinjayar muku su, domin ku kore su, ku hallaka su nan da nan kamar yadda Ubangiji ya alkawarta muku.


“Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya kore su daga gabanku, kada ku ce a ranku, ‘Ai, saboda adalcinmu ne Ubangiji ya kawo mu mu mallaki ƙasar nan.’ Gama saboda muguntar al'umman nan ne Ubangiji ya kore su a gabanku.


Ya kuma aika zuwa ga Kan'aniyawan da suke gabas da yamma, da Amoriyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Yebusiyawa da suke ƙasar tuddai, da Hiwiyawa da suke zaune a gindin Dutsen Harmon a ƙasar Mizfa.


Da kuka haye Urdun, kuka zo Yariko, mutanen Yariko kuwa suka yi yaƙi da ku, haka kuma Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Kan'aniyawa da Hittiyawa, da Girgashiyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, amma na ba da su a gare ku.


Joshuwa kuma ya ƙara da cewa, “Ta haka za ku sani Allah mai rai yana tsakiyarku, ba makawa kuwa zai kori Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Hiwiyawa, da Ferizziyawa, da Girgashiyawa, da Amoriyawa, da Yebusiyawa a gabanku.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan