Ubangiji, wanda yake mulkin Isra'ila, ya kuma fanshe su, Ubangiji Mai Runduna, yake faɗar wannan, “Ni ne farko, da ƙarshe, Allah Makaɗaici, Ba wani Allah sai ni.
Ya jama'ata, kada ku ji tsoro! Kun sani tun daga zamanin dā can, har zuwa yanzu, Na faɗa tun da wuri abin da zai faru. Ku ne kuwa shaiduna! Ko akwai wani Allah? Ko akwai wani Allah mai iko da ban taɓa jin labarinsa ba?”
Iliya kuwa ya zo kusa da jama'a ya ce, “Har yaushe za ku daina yawo da hankalinku? Idan Ubangiji shi ne Allah, to, ku bauta masa, in kuwa Ba'al ne Allah, to, ku bauta masa.” Mutane duk suka yi tsit, ba su ce uffan ba.
Sai ya amsa ya ce, “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan ƙarfinka, da dukkan hankalinka. Ka kuma ƙaunaci ɗan'uwanka kamar kanka.”
Sa'an nan suka yi wannan addu'a, suka ce, “Kai kaɗai ne Ubangiji, ya Ubangiji, Kai ne ka yi samaniya da taurari da sararin sama. Kai ne ka yi ƙasa, da teku, da kowane abu da yake cikinsu, Ka ba dukansu rai, Ikokin samaniya sun rusuna suna maka sujada.