Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 5:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Kada ka yi musu sujada, ko ka bauta musu, gama ni Ubangiji Allahnka, Allah mai kishi ne, nakan hukunta 'ya'ya, da jikoki saboda laifin iyaye waɗanda suka ƙi ni.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Ba za ka rusuna musu, ko ka yi musu sujada ba. Gama Ni, Ubangiji Allahnka, Allah ne mai kishi, nakan hukunta ’ya’ya saboda zunuban iyaye har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suka ƙi ni.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 5:9
13 Iomraidhean Croise  

Ubangiji ya yi alkawari da 'ya'yan Yakubu, ya kuma umarce su kada su yi wa gumaka sujada ko su durƙusa musu, ko su bauta musu, ko su miƙa musu hadayu.


“Ba za ku yi wa wani allah sujada ba, sai dai ni, gama sunana Mai Kishi, gama ni Allah mai kishi ne.


Ni ne mai nuna ƙauna ga dubbai, mai gafarta mugunta, da laifi, da zunubi, wanda ba zai kuɓutar da mai mugunta ba, amma saboda laifin iyaye nakan hukunta 'ya'ya da jikoki har tsara ta uku da ta huɗu.”


Kakan nuna madawwamiyar ƙauna ga dubbai, amma kakan hukunta wa 'ya'ya saboda laifin ubanninsu. Ya maigirma Maɗaukaki, Allah, sunanka kuwa Ubangiji Mai Runduna.


‘Ubangiji mai jinkirin fushi ne, mai yawan ƙauna, kana gafarta mugunta da laifi, amma ba za ka ƙyale mai laifi ba, gama kakan ɗora wa 'ya'ya alhakin muguntar iyaye, har tsara ta uku da ta huɗu.’


don kada ku yi mugunta, ku sassaƙa wa kanku wata siffar kowane abu, ko siffar mace ko ta namiji,


Gama Ubangiji Allahnku wuta ne mai cinyewa, shi kuma mai kishi ne.


gama Ubangiji Allahnku wanda yake zaune a tsakiyarku, mai kishi ne, don kada Ubangiji Allahnku ya husata, ya shafe ku daga duniya.


Amma a fili Ubangiji yakan yi ramuwa a kan maƙiyansa, yakan hallaka su. Ba zai yi jinkirin yin ramuwa a kan maƙiyinsa ba, zai yi ramuwar a fili.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan