Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 5:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Ni ne na tsaya a tsakanin Ubangiji da ku a lokacin don in faɗa muku maganar Ubangiji, gama kun ji tsoro saboda wutar, ba ku kuma hau dutsen ba. “Ubangiji ya ce,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 (A wannan lokaci na tsaya tsakanin Ubangiji da ku, don in furta muku maganar Ubangiji, domin kun ji tsoron wutar, ba ku kuwa hau dutsen ba.) Ya ce,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 5:5
15 Iomraidhean Croise  

Sa'an nan mutanen suka juya daga nan, suka nufi Saduma, amma Ibrahim ya tsaya a gaban Ubangiji.


Ya kawar da wuraren tsafi na kan tuddai, ya rurrushe ginshiƙai, ya sassare siffar Ashtoret. Ya kuma farfashe macijin tagulla wanda Musa ya yi, gama har zuwa lokacin jama'ar Isra'ila suna miƙa masa hadaya ta turaren ƙonawa. Aka ba macijin suna Nehushatan.


Saboda wannan Allah ya ce zai hallaka jama'arsa, Amma Musa, zaɓaɓɓen bawansa, ya yi godo ga Allah, Allah kuwa ya huce, bai hallaka su ba.


A safiyar rana ta uku aka yi tsawa, da walƙiyoyi, da girgije mai duhu a bisa dutsen, aka tsananta busar ƙaho, sai dukan jama'ar da suke cikin zango suka yi rawar jiki.


Ubangiji ya ce wa Musa, “Sauka, ka faɗakar da jama'ar, don kada su ƙetare kan iyakar, su zo garin a kalli Ubangiji, da yawa daga cikinsu kuwa su mutu.


Sai Musa ya sauka wurin jama'a ya faɗa musu.


Sarkinsu zai zama ɗaya daga cikinsu, Mai mulkinsu kuma zai fito daga cikinsu. Zan kawo shi kusa, zai kuwa kusace ni, Gama wane ne zai yi ƙarfin hali ya kusace ni? Ni Ubangiji na faɗa.


Ya kuwa tsaya a tsakanin matattu da masu rai, annobar kuwa ta tsaya.


To, mece ce manufar Shari'a? Ƙari aka yi da ita don fitowa da laifi fili, har kafin na zuriyar nan ya zo, wanda aka yi wa alkawarin, an kuma ba da ita ta wurin mala'iku ne, ta hannun matsakanci.


Kai, ka matsa kusa, ka ji dukan abin da Ubangiji Allahnmu zai faɗa, sa'an nan ka mayar mana da dukan abin da Ubangiji Allahnmu ya faɗa maka. Za mu ji, mu kuma aikata.’


Domin Almasihu bai shiga wani wuri tsattsarka da mutum ya yi ba, wanda yake sura ne kawai na gaskataccen, a'a Sama kanta ya shiga, domin yă bayyana a gaban zatin Allah a yanzu saboda mu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan